Ticker

ABUBUWAN DA AKA HANA GA MAI NIYYA YIN LAYYA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene a ka hana wanda yake da niyyan yin layya aikatawa? shin kuma hanin ya shafi sauran iyalanshi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Daga Ummu Salamah (R.A) cewa Manzon Allah ﷺ ya ce:" Idan kuka ga jinjirin watan Zhul hijjah kuma ɗayanku yana da nufin ya yi layya, to ya kame daga aske gashinsa da kuma yanke ƙumbarsa. Muslim.

A wata riwayar: "Kar da ya cire gashinsa ko wani abu na fatan jikinsa.

Shaykh Muh'd Saleh Al'Uthaimeen ya ce: "Wannan hukuncin ya keɓanci wanda zai yi layyan ne, amma wanda yi mishi layyan za a yi to ba shi da alaƙa da wannan, domin Manzon Allah ﷺ cewa yayi: "Kuma ɗayanku ya yi nufin yin layya.." bai ce: ko za a yi mishi layya ba, kuma saboda Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yin layya wa iyalansa amma ba a naƙalto cewa ya umarcesu daga kamewa daga wannan ba(yanke ƙumba/farce ko fitar da gashi).

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments