Ticker

AMBATON SUNAN MAI LAYYA BA WAJIBI BA NE A LOKACIN YANKA!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Allah ya kara wa malam lafiya, idan mace za ta yi layya tun da ba ita za ta yanka ba ya za ta yi wurin niyya ko sai ta fada wa mahaucin da zai yanka mata?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu. Amin na gode. 'yar uwa abin da yake Sunnah a lokacin yanka dabar layya shi ne:

بسم الله، والله أكبر، اللهم هذا منك ولك، هذا عني.

Kamar yadda hadisin da Imam Attirmizhiy ya ruwaito ya nuna hakan a hadisi mai lamba ta (1521), da kuma wasun Attirmizhiy.

Idan kuwa ya kasance mutum yana yanka ma waninsa ne zai ce ne:

هذا عن فلام

a daidai wurin

عني

 ɗin can, sai kuma ya ƙarishe addu'ar da cewa:

اللهم تقبل من فلان وآل فلان

sai ya ambaci sunan mai layyar a madadin kalmar 'فلان' ɗin nan.

'yar uwa abin da yake wajibi dai kawai shi ne mutum ya ambaci sunan Allah ya ce;

بسم الله، والله أكبر

(Bismillah, Wallahu Akbar)

Abin da duk ya ƙaru a kan wannan faɗinsa Mustahabbi ne ba wajibi ba ne. Saboda haka ko ba a ambaci sunan mai yin layya ba a lokacin yin yankar, to babu laifi, layya ta inganta, Allah ya san niyyar mai yin layyar.

Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 

Post a Comment

0 Comments