Bambancin Ɗan Musulmi Da Ɗan Kafiri

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Malam dan Allah ya bambancin diyar musulmi da na kafuri?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, Malamai sun yi saɓani game da matsayin ‘ya’yan waɗanda ba musulmi ba ta fuskar matsayinsu a duniya da kuma matsayin su a lahira.

Daga cikin abin da malamai suka ce shi ne: matsayin ɗa yana bin iyayensa ne, idan kafirai suka haifi yaro, to wannan yaron yana bin su ne a hukuncin al'amuran duniya, wato ko mutuwa ya yi ba za a yi masa sallah ba, kuma ba za a birne shi a maƙabartar Musulmai ba, Amma matsayinsu a lahira wasu malaman sun ce za a yi masu jarabawa ce, idan suka yi wa Allah biyayya a kan wannan jarabawar sai a sa su a Aljannah, idan kuma ba su yi biyayya ba sai a kai su akasin Aljannah, wato kamar hukuncin waɗanda saƙon Manzanci bai zo masu ba kenan (Ahlul Fatra).

Wato dai matsayinsu a duniya ana riskar da shi ne da matsayin iyayensu, amma a haƙiƙanin lamarin su ba kafirai ba ne, lallurar raino ce ta sa su a ƙarƙashin kafirai, saboda yaro ba zai iya rayuwa ba tare da mai raino ba.

Akwai kuma malaman da suke ganin idan ‘ya’yan kafirai suka mutu kafin balaga, to Aljannah za a sa su, hujjarsu ita ce tun da Annabi ﷺ ya ce: "Duk wani abin haihuwa ana haifansa ne a kan Musulunci, sai iyayensa su mayar da shi Bayahude, ko Banasare, ko Bamajushe".

Bukhariy (1385), Muslim (2658).

Don ƙarin bayani a kan wannan sai a duba Ahkámu Ahliz Zhimma, na Ibnul Ƙayyim.

Su ko ‘ya’yan Musulmai ai duk matsayinsu da hukuncinsu irin na musulmai ne a duniya da lahira.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments