Ticker

Bori A Matakin Magani: Tsokaci Daga Adabi

Hausawa al’umma ce da ta ginu bisa matakan rayuwa har guda uku. Da farko Hausawa sun gudanar da rayuwarsu bisa tsarin al’adun gargajiya wanda ya fara tun daga haifuwa da aure da kuma mutuwa. Hatta bautarsu a gargajiya suka gudanar da ita a wannan matakin. Haka kuma sun gudanar da rayuwa bayan karɓar addinin musulunci duk da haka ba su watsar da al’adunsu na gargajiya ba. Bayan zuwan turawan mulkin mallaka rayuwarsu ta gudana bisa sabon tsari. Duk da waɗannan sauye-sauyen matakan rayuwa bai sa su Hausawa sun watsar da al’adunsu ba. Bori yana daga cikin hanyar gargaji da Hausawa suka ɗauka a matsayin hanyar warakar da al’ummarta. Aikin daga ƙarshe zai duba waye Bahaushe, sannan ya duba ma’anar Bori,da kuma ma’anar magani tare da duba mene ne adabi. A duba ma’anar Bori a taskar adabi, kamar waƙar baka da Karin magana da sauransu.

Bori A Matakin Magani: Tsokaci Daga Adabi

Muhammad Abubakar Zabi
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
08136844199
muhammadabubakarzabi@gmail.com

DA

Adamu Halilu
Sashen Nazarin Harsunan Afirka
Jami’ar Amadu Bello, Zaria
08032307714

Bori

1.0 Gabatarwa

            Hausawa al’umma ce da ta ginu wajen riƙo da al’adunta. Haka kuma, akwai hanyoyi da dama da za a iya duba ire-iren al’adun Hausawa, ɗaya daga cikin hanyoyin ita ce hanyar nazarin Bori na gargajiya wanda suke amfani da shi tun matakin rayuwar farko har ya zuwa wannan zamani da kuma irin tasirin zamanin da aka samu a cikin harƙar Bori a yau.

Daga cikin al’adun gargajiya na Bahaushe, babu wani ɓangare da ya samu karɓuwa, da farin jinni ga manazarta ýan ƙasa da na waje kamar Bori. Rubuce-rubucen da aka yi kan Bori sun fi kowane rubuce- rubuce yawa a fannonin nazarin al’ada. Bunza (2015).

Bori wani nau’i ne daga cikin sassan addinin Bahaushe, watau Tsafi da camfi da kuma Bori. Don haka wannan nau’i na Bori ya samu karɓuwa a wajen Hausawa sosai, suna amfani da Bori a matsayin wata hanya ta samun magani, ko wata hanya ta bauta.Bunza (2015).

            Bori dai a nahawun ma’ana, Kalmar ta ci sunanta. A farfajiyar adabi ba ta tsallake ma’anar wasaba. A ɓangaren al’ada kuma wata hanya ce wadda al’ummar Hausawa suka yi Imani da ita Bunza (2015).

Aikin daga ƙarshe zai duba waye Bahaushe, sannan ya duba ma’nar Bori. Da kuma ma’anar magani tare da duba mene ne adabi. A duba ma’anar Bori a taskar adabi, kamar waƙar baka da Karin magana da sauransu. Sannan sai a kammala aikin.

2.0 Asalin Hausawa A Taƙaice

Sanin asalin Bahaushe kundi ne mai faɗin gaske. Domin Bahaushe mutum ne mai daɗaɗɗen tarihi bisa doron ƙasa. Masana da dama sun ambaci haka akan wa za a kira Bahaushe. Masana ilimin kimiyyar harshe da tarihi da al’ada sun sha gwagwarmaya wajen gano wane ne Bahaushe. Haƙiƙa an daɗe ana ɗauki ba daɗi wajen bin diddigin gano Bahaushe na asali. Daga cikin irin waɗannan masana ilimin harsuna akwai, Schuh da Yalwa (1993) sun bayanna cewa:

Hausawa na a yammacin Tafkin Chadi ne, amma sun warwatsu a wurare daban-daban. Daga cikin wannan akwai Arewacin Nijeriya da Nijer da Chadi. Haka kuma, Harshe ne da ya bunƙasa wajen kasuwanci a ƙasashen Afrika ta yamma, da Afrika ta tsakiya da kuma ɓangaren Arewa maso Yamma da Sudan.

 

Jinju, (1985) a nasa binciken ya ce:

 Mutanen Masar baƙar fata ne kuma sarakunansu (Fir’aunoni ne), baƙaƙe ne har lokacin sarautar gida na ashirin da huɗu. Su waɗannan mutanen Masar su ne a ganina suka yiwo ƙaura zuwa Afirka ta yamma suna zaune a bakin tafkin Chadi wanda can da maƙil yake da ruwa. A wannan lokaci ne mutanen farar fata suka riƙa kai masu hari, sai suka yi ƙaura suka canza wurin zama tare da harshen su na misiranci wanda ya canza ga tarihi ya koma Hausa.

            Duka waɗannan bayanai ba su isa su tabbatar muna da asalin Hausawa da harshensu ba. Domin harshe kaɗai ba iya tabbatar da asalin mutum. Zancen zaman Hausawa a gaɓar Kogin Chadi da alaƙar harsunan gidan Chadi wani wuri ne da Hausawa suka zauna na ɗan lokaci, daga baya suka canza wurin zama.

Haƙiƙa Smith ya ce, wani abu game da wane ne Bahaushe, kasancewar kowane Bahaushe yana iƙirari da harshensa na Hausa a matsayin asali. Hausawa da dama sukan yi kamannu da junansu. Ra’ayin Smith ya so ya yi kama da na Adamu (1978) da yake cewa:

Hausawa ne daɗaɗɗun mazauna Hausa da dukkanin zuriyarsu ta fuskar maza, ko kuma waɗanda suke amfani da al’adun Hausawa da riƙe harshensu da addininsu.

Shi kuwa Bunza (1990) ya bayyana cewa:

Hausawa dai mutane ne da suke zaune a ƙasar Hausa tun 

                        farkonta, kuma suna da zuriya a cikinta har ya zuwa yau

Kazalika, suna magana da harshen Hausa ba su da wani

Harshen in ba Hausa ba, suna da ɗabi’u da al’adu irin na

Hausawa. Idan sun saɓa haka to barbarar yanyawa ne.

Kamar yadda muka gani cewa masana sun kawo wane ne Bahaushe: Bisa ga yadda masana da manazarta suka ce za mu iya cewa, Bahaushe shi ne, mutumin da yake zaune a ƙasar Hausa, ta fuskar launi kuma baƙi ne; kuma iyayensa Hausawa ne, idan kuma ba a ƙasar Hausa yake zaune ba, ya kasance yana jin Hausa, kuma wasu al’adun Hausawa sun yi tasiri a gare shi, to wannan shi ne Bahaushe.

 

 

2.1 Ma’anar Bori

Yana da kyau kafin a fara kallon ma’anar Bori, mu kalli Kalmar Bori. Kalmar Bori takan ɗauki ma’anoni daban-daban idan aka sarrafa ta yadda al’umma ke kallon ta. Bahaushe ya samu Kalmar Bori daga Kalmar “Bore”, Bore na nufin zanga zanga ta fito-na-fito, da nuna rashin yarda, da burin ta’adanci, domin ramuwar gayya, ko tawaye, ga wandaba a so, ko zanga-zangar tabbatar da wanda ake so. Wasu suna ganin daga nan ne aka samo Kalmar bori. ( Bunza 2006:21)

A wata fassarar kuwa, ana hasashen Kalmar bori daga Borin tukunya, ko tuwo, ko fura, ke yi idan an ɗora ta a kan wuta ana girki. Yayin da ruwa suka tafasa zafi ya ci ƙarfinsu suka fara zaɓarɓaka, za a ga dahuwar/girkin ta shiga wasu halaye kamar haka.

-          Za ta ture marfin da aka rufe.

-          Ruwan za su fito waje da ƙarfi.

-          Za ta riƙa fitar da kumfa.

-          Wutar za ta mutu ta kowane gefe..

Idan girki ya shiga wannan halin, za a kira mai shi a ce zo da sauri tukunyarki ta fara Bori. Komai tafasar da ta yi idan ba a samu abu biyu ba, ba a cewa ta yi Bori.

-          Faɗuwar marfi ƙasa

-          Fitar kumfa a bakin tukunya

Haka yake ko a wajen ɗan Bori, matuƙar bai kai ƙasa baki na fitar da kumfa ba, ba a cewa an hau bori. Wata ƙila daga nan ne kalmar ta samo asalinta.( Bunza 2006:21)

2.1.1 Bori

Wani nau’i ne da yasa mu karɓuwa a cikin al’ummar Hausawa sosai. Haka kuma shi wannan fage ya samu karɓuwa a ɓangaren masana da manazarta na cikin gida da waje. Ga kaɗan daga cikin wasu ma’anonin Bori:

“Bori shi ne, shigar Iskoki a ɗayan gaɓoɓin

hanci ko baki ko kunne tare da haƙiƙance

bayyanar su a idon mai bori. Yawo da ake yi

da kai da rawar da ake yi da fizge-fizge hannaye

da gaɓoɓi na fitar hankali su ne bori”(Bunza 2015:19).

Haka kuma ya ƙara da cewa:

 “Bori dai wani wasa ne na gargajiyar Bahaushe

da ya keɓanta ga wasu ýan tsirarru da ke da

  sha’awar kwaikwayar ɗabi’un Iskoki da hulɗa

da su. shigan Iskoki na haƙiƙa, ya wuce bori,

ya zama wata lalura ta daban. Don haka bori ba

haƙiƙa ba ne kwaikwayon shigan iska na haƙiƙa ne”(Bunza 2015:21).

Wata ma’ana ta Bori kuma:

“Bori wata dabarar warkarwa ce da Bokaye suka

yi fice da ita.(Bunza 2015:27).

Ƙamusun Hausa ya ba da ma’anarta

         da dogaro da wata iska wadda wasu mutane ke gaskatawa

don su sami magani da biyan buƙata.(CNHN 2006:50)

Bisa waɗannan ma’anoni da muka gani game da Bori, za a ƙara ganin cewa lallai bori wani fage na musamman wanda ake yinsa bisa wasu dalilai da daman-daban. Mun fahimci bori ana yin sa saboda neman Iskoki, da kuma wasa na nishaɗi, tare da mata ma suna yinsa domin isar da wani saƙon da yake damunsu. Haka kuma yake ana bori domin neman waraka, wato neman magani ga wata cuta da ta damu al’umma.

Don haka za mu iya cewa, Bori wani wasa ne da al’ummar Hausawa ke yi, ta hanyar amfani da garaya da gurmi da goge, tare da ka-ca-kau-ra, da rawa ta fitar hankali, domin nishaɗantarwa, da kuma nema magani ga wata cuta da ta addabi mutum. Tare da yadda mata ke yin amfani da Bori domin isar da saƙonsu ga wanda ya matsa musu, ko ya dame su ga wani lamari na daban. Da kuma neman Iskoki don samun abokan hulɗa.

2.2 Magani

Wannan fage na magani ya samu kulawar masana da mazarta ainun, wanda suka yi ta bayani game da ma’anar magani. Ga kaɗan daga ciki.

“Maganin gargajiya- shi ne yin amfani da itatuwa

                       ko rubutu ko addu’a ko sulkulle, don warkar da

 wata cuta, ko neman wani amfani, ko gusar da

sharri, ko haddasa wani abu saboda biyan buƙata”. (Adamu 2014:125)

 

“Magani shi ne duk wani abu da za a yi, kowata

                       hanya, ko kuma wata dabara da ake yi don gusar

da wata cuta daga jikin mutum ɗungurungum,

                       ko kuma kwantar da ita don kawo jin daɗi ga jiki

                       ko ga zuciya dan sauwaƙa duk wahala da damuwa

                      da ita cutar kan iya haifar Ahmad”, (1984:6).

 

             “Magani- wata hanya ce ta warkar da ko

kwantar da ko rage wata cuta ta ciki ko ta

waje ko wadda aka samu ta haɗari ko kuma

neman kariya ga cuta ko abokan hamayya ko

neman ɗaukaka ta daraja ko ta buwaya ta hanyar

siddabaru da sihirce- sihirce na ban al’ajabi” (Bunza, 1990).

Kamar yadda masana da mazarta suka yi ta faɗi-ta-shi wajen kawo ma’anar magani, za mu iya cewa magani shi ne, duk wata hanya da mutum ya bi wajen yaye wata damuwarsa, da ta dami shi. Walau ta jinya ko ta buƙatun rayuwa.

3.0 Ma’anar Bori A Taskar Adabi

Adabin babbar fitila ce ta hasko rayuwar al’umma da yadda take tafiyar da ita. (Bunza 2015:12).

Haka kuma Ɗangambo, ya ƙara da cewa Adabi shi ne madubi ko hoton rayuwar al’umma. Wannan ya ƙunshi yadda al’adunsu, ɗabi’unsu, harshensu, halayyar rayuwarsu da abincinsu, tufafinsu, maƙwancinsu, hulɗoɗinsu, tunaninsu da ra’ayoyinsu da sauran abubuwa da suka shafi dabarun zaman duniya don ci gaba da rayuwa; kai har ma da abubuwa da suka shafi mutuwa. Duk wata al’ada da ake nazari kan al’umma yana da kyau a lalube adabi a ji yadda ya Harare batun. A nan muna son mu duba Bori ne mu ga me adabi yace game da shi, kamar waƙa da kirari da Karin magana da sauran ɓangarori na adabi.

3.1 Bori A Riwayar Mawaƙan Baka

Mawaƙan baka, adabi Bahaushe suke ƙara faɗaɗa wa ma’ana, da ƙara fito da shi yadda yake a cikin rayuwar al’umma. Domin nuna halin da ake cikin ko yadda al’umma suke. Ana samu Mawaƙa da dama sun yi waƙa a kan Bori, akwai Mamman Shata da Sa’adu Bori da wasu Mawaƙa da dama. Haka za mu ga yadda mawaƙan baka suke tabbatar mana da cewa lallai Bori nau’i ne na Magani, wanda mutum yake nema domin biyan wata buƙata ta daban. Watau jinya ko wata buƙata ta rayuwa. Ga wani misali a lokacin da ƙwaro daga cikin ƙwarin Gambu mai waƙar ɓarayi ke neman sa’a a kashe masa Tsoho Tudu cewa ya yi:

Jagora:       An yi bori, an yi bori, an yi bori

:Na yanka awakina da kaji

:An ce sa’a ta samu babba

:Y ac ce “Dogon zango nab biyo Tudu”

:Wai shi ya biyo Tsoho dag Gyalange.

Magani idan aka duba abin da ka faɗi a nan, za a fahimci cewa lallai bori wani nau’i ne na magani, domin ya nuna cewa ya nemo sa’a a wajen ýan bori. Ya ce ya yanka awaki da kaji domin neman dacewa.

Haka kuma domin sake tabbatar da lamarin bori yana cikin nau’i magani, ga wani ɗiyan waƙa da Narambaɗa yake yi wa wani ɗan sarauta da ya yi takara. Yana cewa:

Jagora:      Ga wani ya kunna ya ga ba ƙafa

  : ýan bori kai shi sun baro

  :Saruru ya baddala abinai

    Yara:      Ya koma biɗan kwabon hura

   Gindi:      Ibrahim na Guraguri

                                   :Maishinkahi bajinin zagi

:Mu dai Allah ya bar muna kaya

Ta kula da wannan waƙar za mu sake tabbatar da cewa bori magani ne, domin ana zuwa nema magani domin wata buƙatar rayuwa. Domin ya kawo cewa shi ɗan takarar ya je neman sa’a wajen ýan bori, suka damfare shi ya zama babu kwabo sai an taimaka

masa. Ke nan Narambaɗa ya nuna cewa ana amsar magani a wajen ýan bori, saboda haka ke nan za mu yarda cewa bori wani nau’u magani ne.

Haka kuma Mamman Shata Katsina ya nuna a cikin bakandamiyarsa cewa lallai bori magani ne, ga misali kamar haka:

Gindi;      Alolo mai ganga ya gode, yaran mai ganga sun gode.

: Ba malamai ba ne,

 :Ba bokaye ba ne,

: Ikon Allah ne,

:Im bori ne,

      :Mai zai hana boka ya yi ɗansa ya samu.

Ya nuna cewa, bori ma wata hanya ce ta neman magani, kamar yadda ya faɗi a cikin waƙarsa. Yadda boka ke bayar da magani in ya isa ya bawa ɗansa ya samu ɗaukaka irin ta sa.

Ga wani misali daga waƙar Ɗankwairo ta Sarkin Gombe yadda yake nuna cewa lallai bori wani nau’i ne na magani, domin ya nuna cewa idan yayan sarakuna suna neman sarauta sukan je gun yan bori domin neman magani ko sa’a gunsu

Sarauta tana wurin Allah

Sarauta tana wurin wanda jallah ya bai girma

Shehu ka biɗa ga Allah ka samu

Sai ga wani ɗan sarkin Gombe bai biɗa ga Allah ba

Ya sai babbakun tumakai

Ya sai babbakun shanu

Sai ya kiraye ýan bori

Kullum ana yi mai bori

Wawa bokaye sun kwashemasa ƙudinsa

Bokaye sun kwace kuɗinsa

Ba shi ga Allah ba shi ga Annabi

Ba shi da tsutsu ba shi ga tarko

Babu kuɗin kuma babu sarauta

Babu kuɗin kuma babu sarauta

Wannan ya nuna cewa yan bori da bokaye suna bayar da magani. Haka kuma Ɗankwairo yana cewa yan bori suna bayar da magani ga waɗanda suke nema. Wannan shi ya ƙara tabbatar mana da cewa lallai bori wani nau’i ne na magani.

3.2 Bori A Riwayar Karin Magana

Karin magana kusan ya mamaye kowane fanni na rayuwar Bahaushe. Yana da wuyar gaske a ce ga sha’anin rayuwar da ba a samun Karin Magana ba, kuma wannan shi ya bada damar kamar yadda harshe da al’ada kan sauya su bi zamani, to kwatankwacin haka Karin magana ke sauyawa. Don haka sau da yawa Karin magana na nuna yadda rayuwar Hausawa take da irin abubuwan da suke mallake da shi, da wanda ba na su ba.

Za mu duba wasu Karin magana da suke tabbatar mana da cewa Bori wani nau’i ne na magani. Ga misali kamar haka:

 An huta Bori ya kashe Boka

           Ina magana? An ce Bori ya kashe Boka

                      Yau da gobe ƙarya ta boka

Duhu ɗakin bori

Ɗakin bori, digar maganin gujajjen bawa

Boka ci kaji, magani sai Allah

Halin bori, halin godiya

Borin girka ba shi warka da mayunwaci

Idan muka duba waɗannan Karin magana za mu fahimci cewa lallai bori wani nau’in magani ne. don yana nuna mafitar lamari ko samun sauƙin abin da ya yi tsanani ko warware wata matsala ko biyan buƙata, da dai sauransu.

3.3 Matsayin Bori A wajen Bahaushe

Bori yana ɗaya daga cikin hanyoyin bauta a lokacin gargajiyar Bahaushe. Baya ga Tsafi da Camfi, sai shi Bori da Hausawa suka yi Imani da shi a wancan lokaci na gargajiya. Wanda wannan hanya ce da ta samar wa Hausawa abubuwa da dama, baya ga hanyar bauta, Hausawa suna amfani da wannan hanya a matsanyin wata hanya ta samar musu da magani, da kuma kariya daga wasu abubuwan cutarwa. Baya ga lokacin gargajiya, Hausawa sun ci gaba da wannan hanya wajen samar wa kansu magani. Wanda daga cikin hanyoyin bautar gargajiya ba hanyar da ta ci gaba da karɓuwa kamar wannan a wajen Hausawa.

4.0 Kammalawa

Wannan aikin bayan an yi gabatarwa an ɗan yi ƙoƙorin kawo waye Bahaushe, sannan ma’anar bori da magani da ma’anar bori a taskar adabi daga ƙarshe kuma bori a riwayar mawaƙan baka, da Karin magana da kuma sanin matsayinsa a wajen al’ummar Hausawa. Wanda nazarin ya tabbatar mana da cewa lallai Bori wani nau’i ne na magani, wanda yake nuna mana irin yadda bori ya yi tasiri a rayuwar al’ummar Hausawa, wanda suka ɗauke shi a matsayin wata hanya ta samar da magani ga al’ummarta. Ta kula da hanyar adabin Hausawa ya ƙara tabbatar mana da hakan, domin a cikin waƙoƙinsu da Karin maganganunsu duk akwai irin waɗannan maganganu da suke tabbatar mana da cewa bori wani nau’in magani ne a ƙasar Hausa.A kowane ɓangare na waƙa da Karin magana an ɗan kawo misalai da za su sake tabbatar mana da haka.

Manazarta

Abdullahi, I. S .S (2012). “Muhallin Magani A Adabin Bakan Bahaushe” A cikin Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 1, Number 4. Department Of Nigeria Languages, Usmanu Ɗanfodiyon University, Sokoto

Adamu T. M (2014). Siddabaru A Ƙasar Hausa. Century publition Ltd, Kano.

Ahmad I. A (1984) Cututtukan ciki da magugunansu” Kundin BA, Sashen Nazarin Harsunan Nijriya, Jamiar Bayero, Kano

Alhassan, H; Musa, U. I da Zarruuk, R. M. (1988). Zaman Hausawa Na Biyu Don Makarantun Gaba Da Firamare. Publications Bureau, Lagos

Bunza, A.M. (1990), Hayaƙi Fid Da Na Kogo: Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa. Kundin Binciken Don Digiri Na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano

Bunza, A. M. (2002). Narambaɗa, Lagos: Ibrash Islamic Publicaiton Centre.

Bunza A. M (2006). Gadon feɗe al’ada.Tiwal Nigeria Ltd, surulere Lagos.

Bunza A. M (2015). “Mene ne Bori? Fashin Baƙin Ma’anarsa cikin Taskar Harshe,         Adabi Da al’ada”. Takarda da aka gabatar a taro na musamman da cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Mutuntar ɗan Adam (CSNLF) Jami’ar Bayero kano ta Shirya mai taken BORI ADDINI KO AL’ADA ranar Talata 16 ga watan yuni 2015 a harabar cibiyar, Mazaunin dindindin.

Ɗanmaigoro, A. (2010) “Magungunan Gargajiya na Hausawa da Fulani”. Cikin Al’adu da Ɗabi’un Hausawa da Fulani”.

Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa, London: Edinburgh University Press, for International Africna Institute.

Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa, Kano: century Research and Publishing Limited.

Gusau, S. M (2014). Diwanin Waƙoƙin Baka: Juzu’I Na biyu, Kano: century Research and Publishing Limited.

Jinju, H. (1985), “Asalin Hausawa Da Harshensa” Maƙala Da Aka Gabatar A Taron Ƙasashen Duniya Akan Hausa Da Adabi Da Al’ada. Jami’ar Bayero, Kano.

Malumfashi I; Ibrahim N. M (2014). Ƙamusun Karin Maganar Hausa. Garkuwa Publications, Kaduna.

Sallau, A.B.S. (2005) “A Sha a yi Wanka, Magani ga ɗan na Gada: Nazari da Tsokaci kan Magungunan Gargajiya na Wanzaman Hausawa a Wannan Zamani” Takarda da aka Gabatar a Sashen Hausa. Dutsin-ma: babbar Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita

Schuh, R.G. and Yalwa, L.D. (1993), Hausa (illustration of the IPA) Journal of the international Phonetic Assocition. 23 (2): 77-82.

Post a Comment

0 Comments