Har yanzu akwai sauran dama ga waɗanda suke da burin shiga shirin DIGITAL FILMMAKING WORKSHOP AND CONTEST KANO 2022.
Kamar yadda aka sani mun buɗe application mun ɗauki wani adadi a baya, wanda a yanzu kuma muna da buƙatar ƙarin wani adadin domin ƙara bunƙasa da shirin ya yi.
Ɗaga taron da kuma neman ƙarin mutanen yana da alaƙa da wani babban shiri na musamman, wanda kuma ya kamata duk wanda ke cikin tsarin a yanzu ya san ya abun zai wakana. Yanzu dai tsarin workshop ɗin ya girma sosai da sosai, domin an tuntuɓi manyan mutane da za su shigo ciki, kama daga daktocin ilmi da farfesoshi. Sannan mun sami sukunin bayar da kyauta ta musamman ga kowanne mutum ɗaya wanda ya kasance a cikin shirin; ba wanda zai shigo ba tare da ya sami kyauta ba.
A wannan karon mun bayar da dama ga dukkan wanda ke son kasancewa a cikin shirin da ya cike application form ɗin ta hanyar shiga link ɗin nan da ke ƙasa.
https://forms.gle/dyYcfmBB92hQSMEr6
-Damarmakin da wanda ya sami shiga shirin zai samu:
1. Koyon sana'a domin dogaro da kai
2. Shaidar ƙwarewa (Certificate) na kammala workshop.
3. Kyautar hard dics, mini laptop, printers da sauran su ga kowanne mutum ɗaya daga cikin shirin.
4. Samun ilimin sanin mene ne film da kuma muhimmancinsa a duniyarmu ta yau.
5. Tarayya da manyan masana fina-finai.
6. Damar zamowa a cikin zakarun da za su sami kyautar Naira Milyan ɗaya.
Abubuwan da ya kamata ka sani kafin ka shiga tsarin:
1. Kwana 4 kacal muka bayar domin cike wannan application ɗin, kuma daga ko'ina mutum yana iya shiga ba iyakancewa.
2. Duk wanda ya cike, za mu saka shi a cikin WhatsApp group namu domin samun saƙonni game da workshop ɗin.
3. Mun ɗaga ranar taron ne daga 20th/06/2022 sannan za mu sanar da sabuwar ranar taro a ranar 26th/06/2022
4. Samun horo daga ƙwararru a kowanne fanni
5. Taron zai gudana ne a cikin birnin kano
6. Shiga tsarin gasa (contest) kyauta ne, workshop ne dole sai an biya kuɗin rajista Naira dubu 3000 kacal.
Sannan sai wanda yake workshop zai sami shiga contest.
Domin sanin abubuwan da za a koyar sai a shiga wannan link ɗin da ke kasa a cika form.
https://forms.gle/dyYcfmBB92hQSMEr6
Sign.
________
Workshop management.
+2348166626264
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.