Falalar Karanta Suratul Kahfi A Ranar Jumma'a

    TA𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Yaushene Lokacin Karanta Suratul Kahafi Ranar Juma'a, Mene ne Falalar Karanta Ta Ranar Juma'ar?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    An ruwaito falalar karanta Suratul kahafi ranar juma'a ko daren juma'ar hadisai ingantattu, daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam daka ciki akwai.

    1- Daka Abu Sa'idul Khudry Allah yaƙara yarda dashi, Ya ce: (Wanda Ya karanta Suratul Kahafi Adaren juma'a Allah Zai haska Masa Haske tsakaninsa da Ɗakin Ka'aba) Darumi (3407), Albani ya Ingantashi a cikin Sahihul Jami'i (6471).

    2-Wanda Ya karanta Suratul Kahafi Ranar Juma'a, Allah zai Haska Masa Haske Tsakanin juma'ar Zuwa wata Juma'ar.

    Hakim ya ruwaito shi (3/399) Da Baihaƙy (3/249) Ibnu Hajar a cikin Takarijin "Azkaar" Ya ce: Hadisine Kyakkyawa, Ya ce: Shi ne Hadisin Da yafi Ƙarfin cikin Abun da Aka ruwaito akan karanta Suratul kahafi ranar juma'a. Duba Faizhul Ƙadeer (6/198) Albani Ya ingantashi a cikin Sahihul Jami'i (6470).

    3- Daka Abdullahi dan Umar Allah yaƙara yarda dasu ya ce:, Manzan Allah Sallalahu Alaihi wasallam ya ce: (Wanda ya karanta Suratul Kahafi ranar juma'a, za a sanya Masa haske A ƙar-ƙashin Ƙafarsa har sama dazai dunga haska Masa ranar Alƙiyama, za a gafarta Masa tsakanin Juma'ar Zuwa wata Juma'ar). Munziri ya ce: Abubakar Bin Mardawaihi ya ruwaito shi, da Isnadin da Babu laifi dashi, a cikin Tafsirinsa, Duba Attargeebu Wattarheebu (1/298).

    Ana Karanta Suratul kahafi a cikin daren juma'a ko a yinin juma'a, daren juma'a yana farawane daka faduwar ranar Alhamis, Ranar juma'a ko Wuninta yana ƙarewa da faduwar ranar juma'ar, .

    Abisa Wannan lokacin karanta Suratul kahafi ranar juma'a yana farawa daka faduwar ranar Alhamis, izuwa faduwar ranar juma'a.

    Manawi Ya ce: Ibnu hajar ya ce: haka ya faru a cikin wasu ruwayoyi "Ranar juma'a" a wasu kuma "daren juma'a" faizhul ƙadeer (6/199).

    Manawi Ya ce: Abin sone Mutum ya karanta ta ranar Juma'a ko daren Juma'a kamar yanda Imamu Shafi'i ya Nassanta. Faizhul Ƙadeer (6/198).

    Ba'a ruwaito hadisai ingantattu ba akan karanta Suratul Ãli Imran ba, ranar juma'a, duk wani hadisi da aka ruwaito akan haka, mai raunine sosai, koma Na ƙaryane.

    Daka Ibnu Abbas Allah yaƙara yarda dasu ya ce: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Wanda ya karanta surar da'a cikinta aka Ambaci Ãli imrana, Mala'iku za suyi ta yi Masa salati har Rana ta fadi). Dabarani ya Ruwaitoshi a cikin "Mu'ujamul Ausad" (6/191). da Kabeer (11/48).

    Hadisin Mai raunine Sosai, Haitami ya ce: dabarani ya ruwaitoshi a cikin "Mu'ujamul kabeer" a cikinsa Akwai Dalha Bin zaid, Mai raunine Sosai. Duba Mu'ujamul zawa'id (2/168).

    Ibnu Hajar ya ce: Dalha mai raunine sosai, Imamu Ahmad da Abu dauda Sun dangantashi cewa yana Ƙir-ƙirar hadisan Ƙarya yana jinginawa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam. Duba Faizhul Ƙadeer (6/199).

    Albani ya ce: Hadisin Ƙaryane, duba hadisi Mai lamba ta (5759) a cikin "Za'iful jami'i "

    Daka ciki Akwai Abun da haitami ya ruwaito, Wanda ya karanta (Suratul Baƙara da Ãli Imrana a daren Juma'a yana da ladan da yawansa yakai tun daka Ƙasan Bakwai zuwa Saman Bakwai)!.

    Manawi Ya ce: Rarraunane Sosai, duba Faizhul Ƙadeer (6/199).

    WALLAHU A'ALAMU.

    Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.