Fitinar Mata

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Dan Allah Ina san Ƙarin Bayani Akan Wannan Hadisin, { Ban Bar Wata Fitina Abayana Ba Wacce Tafi Cutar Da Maza Kamar Fitinar Mata Ba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله العزيز المنان.

    Wannan hadisin shi ne hadisin Usama bin Zaid Allah yaƙara yarda dasu wanda Bukhari (5096) da Muslim (2740) Suka ruwaitoshi.

    Saboda Mace ita ce abar kallan Maza, Allah ya dorawa namiji ya halittaceshi akai ya sanya masa sha'awar karkata zuwa ga mace, yaso ko baiso ba, wannan al'amarine da'aka halicci namiji a kansa, mace ita ce abar jin daɗin namiji, idan ya kalleta jijiyoyin kai saƙo zuciyarsa za su motsa, saboda haka shari'a ta Umarceshi ya runtse ganinsa,

    Zuƙata suna shaƙuwa da leƙawa zuwa sha'awar mace, Allah ya sanyawa matune sha'awowi kamar yanda ya ce:

    ﺯُﻳِّﻦَ ﻟِﻠﻨَّﺎﺱِ ﺣُﺐُّ ﺍﻟﺸَّﻬَﻮَﺍﺕِ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎﺀ ﻭَﺍﻟْﺒَﻨِﻴﻦَ ﻭَﺍﻟْﻘَﻨَﺎﻃِﻴﺮِ ﺍﻟْﻤُﻘَﻨﻄَﺮَﺓِ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺬَّﻫَﺐِ ﻭَﺍﻟْﻔِﻀَّﺔِ ﻭَﺍﻟْﺨَﻴْﻞِ ﺍﻟْﻤُﺴَﻮَّﻣَﺔِ ﻭَﺍﻷَﻧْﻌَﺎﻡِ ﻭَﺍﻟْﺤَﺮْﺙِ .{ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ 14 }

    Mun ƙawatawa mutane son Ababen sha'awa daka mata da 'ya'ya da kayan ƙyale ƙyale na dinare da Azurfa.

    'ya'ya suna zuwa daka mata, hakan kuma baya samuwa saida jima'i, mata sune mafi girman fitina saboda haka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Duniya Abace mai zaƙi mai kwarran shukoki ababen ƙaye wajan kallo, Allah ya sanyaku a cikinta yaga yaya zakuyi aiki, kuji tsoran duniya kuji tsoran mata, domin farkon fitinar data samu Banu isra'ila tasame sune ta hanyar mata.

    Muslim (2742).

    Haduwar mata da maza da chakuduwarsu awajan aiki ko kasuwa fitinace mai girma, saboda Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce: Mace idan ta fuskanto namiji tana fuskantoshi ne asifar Shaiɗan, haka idan ta juya masa baya.

    Turmuzi (1158) da ibnu hibban a cikin Sahihin littafinsa (5572) Albani ya ingantashi a cikin sahihul jami'issageer (845)

    Shi ya sa zakaga duk inda namiji yake Hankalinsa ya kan mace, akan hanyane a kasuwane awajan aikine da sauran gurare, ko akafafen internet zakaga inda hoton mace anfi rububin zuwa wajan campanoni Sunfi amfani da hotunan mata, kai hatta mutumin dayake hatsabibi akesan shammatarsa sai abi kowacce hanya yagagara amma da Anbi ta hanyar mace cikin ƙan-ƙanin lokaci za'aci nasara a kansa.

    Haka idan mutum jarumine tsayayye idan baiyi taka tsan-tsan ba sai kaga anyi amfani da mace an rusa shi.

    Koda ƙasashen musulunci da musulamai da'akasan akwai sauran ruhin musulunci atare dasu kuma shugabanninsu suna da Addini gwar-gwadon hali, ba'aci nasara a kansu ba saida akabi tahanyar mata tsala-tsala aka aura musu.

    Shi ya sa Namiji idan yai Aure baya kubuta daka halaye guda uku.

    Wani bayan ya yi aure yake samun kansa cikin tasku da kidimewa, macen dazata rikita masa hankalinsa tazo, Musamman idan kyakkyawace bata tsoran Allah, ba zai iya ƙin yi mata duk Abun da ta nema ba, shiyasa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Ban taɓa ganin mai tauyayyen hankalin da yake tafiya da hankalin namiji jajirtacce kamar mace ba.

    Bukhari (1462) da Muslim (79).

    Wanda yake wanzuwa ahalin da yake kafin Aure, Amma kaɗan ne idan yasamu mace mai tsoran Allah, saliha mutuniyar kirki.

    Inko bai samu wannan ba, zata dunga shagaltar dashi ne, yau daukeni muje rastuarant kaza, yau muje gidan zoo, gobe muje super market, jibi mutafi wajan shaƙatawa, zata shagaltar dashi daka komai sai hutun kanta dajin dadinta, wannan fitinace.

    Shiyasa Allah Madaukakin Sarki ya ce:

    إِﻥَّ ﻣِﻦْ ﺃَﺯْﻭَﺍﺟِﻜُﻢْ ﻭَﺃَﻭْﻟَﺎﺩِﻛُﻢْ ﻋَﺪُﻭًّﺍ ﻟَّﻜُﻢْ ﻓَﺎﺣْﺬَﺭُﻭﻫُﻢْ {ﺍﻟﺘﻐﺎﺑﻦ 14.}

    Lallai A cikin matayenku da 'ya'yanku akwai waɗanda fitinace ku kiyayesu.

    Ibnu Ƙayyeem ya ce: Wannan adawar bata ƙiyayya dajin haushi bace, ƙiyayyace wacce tushenta shi ne so da tausayi, idan zakai sallah tace kazauna taganka kadauke mata kewa, idan zaka fita tace in kafita hankalinta tashi yake tsoro takeji, idan zaka neman ilmi tace ina zakaje, zaka barni nikadai a gida ina shiga ƙunci, idan zai umara ta hanashi idan zai aikin hajji tahana, idan zai kyautatawa 'yan'uwansa ta hana, duk wani aikin alkhairi idan zai yi sai ta hanashi, aƙarshe sai kaga wannan ƙiyayyar tazama kamar ƙiyayyar bakin ciki dajin haushi. Sai Mutum yawayi gari yanada ƙarancin ayyukan alkhairi, duk saboda mace ko dah.

    Amma Allah baice dukkan Mata ko 'ya'ya ba, wasu daka cikin mata da 'ya'ya ba haka sukeba, daka cikin mata akwai wacce ita ce take gyara namiji, ita ce take umartarsa da ayyukan Alkhairi tana hanashi aikata mummuna, wani lokacin yanaƙi wani kuma ya Amsa, ba dukkan mata ko 'yaya ne suke zama fitina ba.

    Namiji idan ya zauna agaban mace kamar yanda ibnu hazam ya ce: jikinsa zai fara motsi kamar kafadarsa da kansa, da idansa ba tare da sonsa ba, saɓanin idan agaban maza yazauna, wannan Abune sananne.

    Wannan fidrace Babu mai ja a kanta sai Namiji mai girman kai,

    Waɗannan Ababe Sune Abun da wannan hadisi yake nufi, (Ban bar wata fitina abayana ba, wacce tafi cutar da maza sama da fitinar mata).

    WALLAHU A'ALAM.

    Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.