Waɗanda ba su karanta rubutu na farko da na biyu ba muddin ba su faro daga kansu ba to ba lallai ne su fahimci wannan kashi na ukun ba. A kashi na biyu na tsaya ne inda nake bayani akan furucin da al'ummar Karai-Karai suke yi na "Yahweh" da kuma "Yahweh, Ndagai nau" wanda bayan na bayyana ma'anar kalmar ta "Yahweh" na kuma faɗi abinda Bakarkarai yake nufi idan aka ji ya faɗi kalmar wanda duk mai karatu ya fahimta cewa akwai alakantuwa ta imani tsakanin Karai-Karai da kuma wannan kalma ta "Yahweh" ɗin wanda shi ne abinda zamu duba a yanzu.
Gargajiya: Nazarin Daɗewar Addini
da Kaɗaita Ubangiji a Tsakanin Al'ummar Karai-Karai (3)
Musaddam Idriss Musa
Marubuci kuma Mai Binciken Tarihi
07067132948
Asalin Kalmar "Yahweh" na
harshen Karai-Karai
Bincike ya kai ni ga samo
tabbataccen bayani akan ainihin inda kalmar Yahweh ta samo asali da kuma farkon
ma'ana ko abinda take nufi kamar dai yadda tarihi ya nuna inda domin yin bayani
cikin gamsassun hujjoji, zamu nazarci kalmar ta fuskar manyan addinai guda biyu
da muke da su a yanzu haka a Najeriya kafin kuma mu ɗora da abinda ya zo daga
rubutaccen tarihi domin abinda bincike ya nuna a game da daɗewar kalmar Yahweh
shi ne cewa an fara amfani da ita ne tun a zamanin ƙarni na 6 Miladiyya wanda
idan muka duba nisan daɗewar zamanin yayi tsufan da idan muna son yin batu akan
sa to dole ne sai mun fara samar da bayanin wani abu da zai sa zukatan mu su
samu nutsuwa akan abinda muke son yin bayani akai wanda domin yin hakan, dole
ne mu yi duba ga neman sanin shin meye ne muka sani game da ƙarni na 6 ko kuma
wane tarihi muke da shi game da wancan zamanin? Domin samun amsar wannan
tambaya dole mu koma ga littattafan addinai domin su ne suke ɗauke da bayanai
akan al'amuran da suka faru daga farkon wannan duniya har izuwa wanda zasu faru
a ƙarshenta.
A duniyar mabiya tafarfin addinin
Musulunci an yi imani da cewa Allah maɗaukaki, ya sauƙar da manzanni da kuma
annabawa masu tarin yawa inda kuma a cikin Alqur'ani mai girma ya ambaci
sunayen guda 25 daga cikin su tare da bada labaransu don al'ummar musulmi na
yanzu su sansu kuma su yi imani da cewa sun wanzu a doran duniya a gabannin
wanzuwar wannan al'ummar tamu ta yanzu. Daga cikin waɗannan annabawa 25, an
kuma samu jerin sunayen 5 a matsayin annabawa mafi girman matsayi a wurin
Ubangiji, inda guda daga cikin su shi ne Annabi Musa wanda wani abin ban
sha'awa game da abinda muke son gabatarwa a nan shi ne, hatta a cikin littafin
mabiya addinin Kiristanci sun yi imanin cewa Allah ya taɓa sauƙar da manzo daga
manzanninsa masu girma da aka ambace shi da suna Prophet Moses wanda kuma shi
manzon da su kuma Musulmi suke kiransa da suna Annabi Musa wanda shi suna Musa ɗin
ya samo asali ne daga Larabci a matsayin harshen da aka sauƙar da Alqur'ani da
shi. Ita kuma kalmar Moses ta samo tushe daga sabon alƙawari (New Testament)
wanda aka samar da shi da harshen Turanci. To, ma shin me yasa nake kawo waɗannan
bayanan? Saboda ƙoƙari muke mu koma ga ainihin lokacin da aka samo kalmar
Yehweh da kuma ma'anarta tare da dubawa mu gani ko tana da bambanci da sanin da
muka yi mata a cikin al'ummar Karai-Karai
Kundin da ake adana rubutaccen
tarihin duniya na Encyclopedia Britannica ya bayyana cewa harshen da aka fara
sanin kalmar Yahweh ta bayyana a cikinsa shi ne Hibraniyanci kuma daga nan ne
asalin kalmar yake farowa wanda shi wannan yaren Hibraniyancin kamar yadda na
bayyana a rubutu na biyu shi ne yare mafi daɗewa a duniya saboda shi ne yaren
da annabawan farko da kuma manzanni suka yi amfani da shi wanda aka bayyana
cewa bayan shuɗewarsa ne aka samui dandazon waɗannan harsunan da muke amfani da
su a yau. Idan muka koma ga Britannica, bayanin ya ɗora da cewa kuma zamanin da
aka fara amfani da kalmar "Yehweh" ɗin a cikin yaren Hibraniyancin
shi ne zamanin ƙarni na 6 lokacin da aka sauƙar da ita ga Annabi Musa (Prophet
Moses) a matsayin sunan Ubangijinsa da zai yana bautawa saɓanin sauran abubuwan
bauta da al'ummarsa ta wancan zamanin suke bautawa wanda a littafin mabiya
addinin Musulunci Surah ta 2 (Baqarah) da bayanin da ta ƙunsa ya kasanceu
babban abin misali na daga ire-iren abubuwan da mutanen wancan lokacin suke
bautawa kuma shi ne dalili na aika musu shi Annabi Musa tare da ita wannan
kalma ta Yehweh kamar yadda bayanin ya zo a matsayin cewa shi ne yadda sunan
Ubangiji wato Allah ya kasance a cikin harshensa na asali domin ita kalmar
Allah asalinta na komawa ne ga harshen Larabci wanda kuma bayyanannen abu ne
dama cewa Annabawa na da waɗanda aka fara aikowa sun fito ne daga wasu al'ummun
waɗanda ba Larabawa ba.
Kenan ashe "Yehweh, Ndagai
nau" ɗin da tsofaffi kuma dattawan Karai-Karai suke faɗa wanda na bayyana
mana abinda yake nufi ma'ana "Ubangiji na, Allah na" abu ne da yake
da asali na daɗewa tare da yin nuni ga irin tafarkin imanin da al'ummar suka
ginu akai.
Sai dai kuma wace hujja ce ake da
ita wadda za ta nuna cewa al'ummar Karai-Karai suna da wata dangantaka ta
harshe da kuma tsohon harshen annabawa na farko ko kuma dai kawai bayanin duk
ya ƙare a hasashe ne? Domin samun wannan amsar sai a biyo ni a rubutu na gaba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.