Haddi A Musulunci 01
Haddi
kankarar zunubi ne ga wanda aka tsayarwa tun anan duniya.
Daga Ubadatu Ɗan Samitin (R.A) Ya ce:
Mun kasance
a tare da Manzon ALLAH {s.a.w} a wani majalasi sai ya ce:
Zakuyimin
alƙawari akan baza kuyi shirka da ALLAH ba, baza kuyi zina ba, ba za kuyi sata
ba, kuma ba zaku kashe ran da ALLAH ya haramta kashewa ba, face sai da gaskiya,
Wanda ya cika wannan alƙawarin daga cikinku,
to ladansa yana wajen ALLAH,
Wanda kuwa ya aikata wani abu daga cikin waɗannan
abubuwa sai akayi masa haddi (hukunci ) a duniya, to wannan shi kankarar zunubi
ne a gareshi.
Wanda kuwa ya aikata ɗaya daga cikinsu, sai
ALLAH ya rufa masa asiri, to lamarinsa yana ga ALLAH, idan yaso ya yi masa rahma,
idan yaso ya yi masa azaba.
Sannan a
wani hadisin kuma Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce: Tsayar da haddi a bayan ƙasa shi
yafi alkhairi ga mazaunan cikinta daga ruwan saman kwana arba'in.
[Nisa'i ne
ya rawaito shi.
Waɗannan
hadisai suna magana ne akan hukunci da littafin ALLAH akan wanda ya aikata ɗaya
daga cikin laifukan da aka lissafo a cikin hadisin dama waɗanda ba a lissafo
ba.
Idan mutum ya aikata zina mai aure ne ko mara
aure, matar aure ce ko buduruwa, saurayinne ko mai aure, sai aka kama mutum,
kuma aka sami shaidu guda huɗu (4) sai alƙali ya tambayesu ɗaya bayan ɗaya,
kuma ko wanne daban, suka tabbatar da sun gansu turmi da taɓarya, kuma bakinsu
ya zo ɗaya, to sai ayiwa wanda aka kama ɗin hukunci.
Wannan hukuncin da aka yiwa mutum na zina ne,
ko na sata ko zinar mai aure ko na kisa, to ana yiwa mutum shikenan, nan take
ALLAH zai kankare masa zunubansa.
Idan kuwa mutum ya aikata laifin zina ko kisa
ko waninsa sai ALLAH ya rufa masa asiri, babu wanda ya ganshi, to kada ya
tonawa kansa asiri, sannan kuma Annabi {s.a.w} yace sakamakonsa yana ga ALLAH
idan yaso ya yafe masa, idan yaso kuma ya yi masa azaba.
Idan kuma mutum ya gaggauta tuba tun anan
duniya, to ALLAH mai jine mai ganine, mutuƙar ka yi tuba mai kyau, ALLAH zai
gafarta maka abinda ka aikata na zunubanka baki ɗaya da wanda ka sani da wanda
baka sani ba.
Babu laifin da ALLAH baya yafewa mutuƙar an
nemi yafiyarsa, sai haƙƙin wani, haƙƙin waninma akwai irin wanda ALLAH yake
yafewa, mutuƙar babu son zuciya da ganganci a cikinsa.
ALLAH ka
bamu ikon aiki da abinda muka karanta.
ALLAH ka
gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu.
Duk mai
neman ƙarin bayani ya yi mana magana ta private.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.