An karɓo daga Ɗan Abbas (R.A) Ya ce:
Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:
Wanda kuka sameshi yana yin aiki irin na mutanen Ludu, to ku kashe wanda ya yi da wanda akayi dashi.
Wannan hadisi kai tsaye yana mana nuni da duk
wanda aka kamashi yana luwaɗi da me yin da wanda akeyi dashi hukuncin kisa
yahau kansu.
Idan ance luwaɗi akwai ta maza akwai ta mata
wato maɗigo, kuma dukkansu hukuncin su ɗaya ne.
Na farko meyinsu ya halatta abin da ALLAH ya haramta, hallata abin da ALLAH ya haramta kuwa kafirci ne, duk
wanda ya halattawa kansa abin da ALLAH
ya haramta ya kafirta.
Yin luwaɗi ko maɗigo da mai dashi sana'a
wannan halatta shi ne, ko da iya laifin halattawar kaɗai hukuncin kisa yana
hawa kan mutum, balle kuma nassi kai tsaye ya nuna akashe meyin da wanda akeyi
dashi.
Yaku masu luwaɗi da maɗigo kuji tsoron ALLAH
ku daina wannan mummunan aiki, lallai abune mai mutuƙar muni, ku tuba wa ALLAH
lallai ƙofar tuba a buɗe take.
Kada ka sake ka koma ga ALLAH kana aikata irin
wannan aiki, ka yi ƙoƙari ka tuba tun anan duniya ka kuma nisanci laifin, za ka
sami dacewa a gurin ALLAH.
ALLAH ka bamu
ikon aiki da abin da muka karanta.
ALLAH ka
gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.