Hakkokin Aure Abisa Alƙur'ani Da Sunnah

     DARASI NA 35

     MAZA INA KIRA GAREKU

    Da yawa daga cikin mazan aure a wannan zamanin inda za ka leƙa wayoyinsu ba za ka rasasu da chat da wasu matan banza a waje ba.

     Da yawansu kuma za ka ga basa so su sami matansu da aikata irin wannan laifin, amma shi yana aikatawa saboda rashin tsoron ALLAH.

     Malamai sun ce baya halatta mace ta rinƙa bincike a wayar mijinta, sai ku kuma maza kuke amfani da wannan hujjar kuke abin da kuka ga dama, kuna chat na batsa, kuna tura hotunan jikinku ga matan banza, suma suna turo muku, shin kuna tunanin kuna yiwa ALLAH wayo ne?

     WALLAHI yadda matarka zataci amanarka ALLAH ya ƙona ta, haka kaima za kaci amanarta ALLAH ya ƙonaka, duk laifin da idan matarka ta yi maka zai jawo mata shiga wuta kaima idan ka yi mata irinsa za ka shiga wuta.

     Kada son kanka ya sa ka ruguza lahirarka, kuma duk yadda kakai da wayo da dabara na kada a gane kana kula matan banza a waje alhali kana da mata a gida, to kaima sai an lalata ‘yarka ko matarka ko mahaifiyarka ko ƙanwarka ko yayarka ko kanaso ko bakaso.

     Sannan kuma tayaya za ka rinƙa bincike a wayar matarka amma kai don an hanasu bincike a wayoyinku sai kuma ku rinƙa zaluntarsu, kuna cin amanarsu, kana tunanin ALLAH zai barka ne?

     Yadda idan matarka taƙi amsa kiranka izuwa makwanci mala'iku za su la'anceta, haka kaima idan ta zo da buƙatarta, kaƙi amsa mata ba tare da dalili na larura ba, ALLAH zai yi fushi dakai, domin yadda kake da haƙƙi a kanta haka itama take da haƙƙi akanka, kuma duk wanda ya tauye haƙƙin wani a cikinku ALLAH sai ya karɓa masa haƙƙinsa.

     Kawai don an baku dama saiku rinƙa abin da kukaga dama, lallai ku sani ALLAH yana sane da abin da kuke aikatawa, kuma kowa zai sami sakamakonsa tun anan duniya, sannan kuma kaje lahira ka haɗu mala'ikun azaba.

    ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.

    ALLAH ka yafe mana zunubanmu baki ɗayanme Ameen.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.