Hanyoyin Rage Tsananin Sha'awa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assslamu alaikum, Malam ko akwai wata magani da zan sha don daina sha'awa ko rageta, Ina da yawan sha'awa abu kadan yeke tada mun sha'awa ko hira Mallam. wllh ina da matsaninciyar sha'awa wanda ko da yaushe ina cikinta shi ne nake tsoron faɗawa halaƙa, don Allah a taimaka ni budurwa ce.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalamu. To da farko dai lallai ki Kamewa daka gane-gane domin kallace-kallacen wasu abubuwa da hotunan tsiraici masu motsi sha'awa yana kai mutum zuwa haram. Idan kina chating da samari mai motsa sha'awa kiji tsoron Allah ki daina. Ki yawaita yin azumi Ki daina hirar batsa da maza ko mata yan'uwanki.

    Ita sha'awa sinadari ce ta musamman wacce Allah ya gineta ajikin Ɗan Adam kamar irin su barci, yunwa, kishirwa, etc. Don haka bata da abinda ke danneta sai dai idan mutum ya tarbiyyantar da zuciyarsa akan guje ma hakan. Kuma ita sha'awa tana daga cikin amanonin da Allah Maɗaukakin Sarki ya ajiye ajikin bayinsa, Kuma ya yi iyakance halastattun wuraren da ake ajiye wannan amanar. Kuma ya yi bayanin cewa waɗanda suka kasa kiyaye wannan amanar, sakamakonsu ita ce Wuta in har basu tuba ba.

    Allah Maɗaukakin Sarki ya gaya ma Manzon Allah ﷺ wata nasiha wacce ya umurceshi ya gaya ma muminai. Yace : "KA GAYA MA MUMINAI MAZA SU RUNTSE IDANUWANSU KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU, WANNAN SHI YAFI TSARKAKA GARESU.. DOMIN ALLAH MASANI NE GAME DA ABINDA SUKE AIKATAWA".

    Kuma Manzon Allah ﷺ ya bama dukkan Samari da 'Yan mata shawara. Yace "YAKU TARON SAMARI!! WANDA YAKE DA IKON ƊAUKAR NAUYIN IYALI TO ya yi AURE. DOMIN SHI (AURE) YAFI SANYA RINTSEWAR IDANU DA KUMA KIYAYE AL'AURA. WANDA BASHI DA IKO KUMA TO ya yi AZUMI DOMIN SHI (AZUMI) TAKUMKUMI NE".

    To kin ga dole sai kin kiyaye idanunki daga kalle-kallen haramun, ki kiyaye zuciyarki daga tunanin saɓa ma Allah, Kuma ki shagaltar da jikinki da zuciyarki wajen yawaita azumi da sauran ayyukan bin Allah. Idan kuma kina da dama da iko to kije kiyi aure kibi sunnar Anmabinka ﷺ shi yafi.

    Ba zai yiwu kina kalle-kallen abinda Allah ya haramta miki ba, sannan ki rika zargin kanki wai kina da Ƙarfin Sha'awa ba. Kowa da kike gani yana da ita ajikinsa. Amma tsoron Allah ne ke sanya kowa ya kiyaye.

    Daga cikin magungunan Musulunci waɗanda ake amfani dasu wajen dakile sha'awa akwai SHAJARATU MARYAM: Bishiya ce wacce ake amfani da ita don magance matsalolin Mata. Amma namiji zai iya sha, tana cire masa sha'awa sosai daga jikinsa da zuciyarsa.

    Ki Yawaita shan Lemon tsami (Idan baki da Olsa). Ko kuma Jar kanwa ('Yar Ƙalilan).

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.