𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne
Hukunci Yawaita Hamma A cikin Sallah.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله رب
العالميين.
Allah ya
yabi bayinsa muminai dacewa sune masu nutsuwa da kushu'i a cikin sallar su,
(الذين هم في
صلاتهم خاشعون
Sune waɗanda
a cikin sallar su, suna tsoran Allah.
Annabi
sallallahu Alaihi wasallam ya ambaci cewa Shaiɗan yana kai kawo dan daukewa
mutum hankali a cikin sallarsa, Allah kuma ya jarrabi muminan dahakan, hanyar
da Shaiɗan yake daukewa mutum hankali asallarsa shi ne ya zo yakawo masa
tunanin abubuwan duniya, dasanya masa kokwanto a cikin sallar sa, daka ciki
akwai tursasawa mumini hamma a cikin sallarsa, Annabi sallallahu Alaihi
wasallam yabada labari cewa hamma daka Shaiɗan ce, kuma ya umarcemu damu mayar
da hamma gwar-gwadon yanda muka samu hali, idan kuma hammar taci karfinmu tomu
sanya hannayen mu akan bakunanmu, ga wasu daka cikin nassoshin da mutum zai yi
idan hamma ta gallabeshi a cikin sallar sa.
Daka abu
sa'idul kudri yardar Allah takara tabbata a gare shi ya ce: manzan Allah
sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Idan dayanku yai hamma awata ruyawar a cikin
salla toya kame hammar karyayita gwar-gwadon ikonsa domin Shaiɗan yana shiga
bakin mutum idan yai hamma) Muslim (2995).
Daka Abu
huraira yardar Allah takara tabbata a gare shi daka Annabi sallallahu Alaihi
wasallam ya ce:(hamma daka Shaiɗan ne, idan dayanku yai hamma yamar dashi
gwar-gwadon yanda zai iya, domin idan dayanku yai hamma yace " Ha"
sai Shaiɗan yai dariya, ) Bukhari (3115) da muslmi (2994).
Ibnu hajar
rahimahulla ya ce:
An jingina
hamma zuwa Shaiɗan ne, saboda yana san yaga mutum yana hamma, domin fuskar
mutum takan canja yayinda ya yi hamma sai Shaiɗan yai dariya, bawai ana nufin
Shaiɗan ne ya yi hammar ba.
Ibnul arabi ya
ce: Ana jingina dukkan wani mugun aiki zuwa Shaiɗan ne domin tahanyarsa aikin
ke faruwa, haka dukkan wani aikin alkahiri kyakkyawa ana jinginashi ga Allah
saboda dataimakonsa yake sanuwa, hamma tana zuwa saboda cika ciki, kasala tana
wanzuwa saboda hamma, hakan nafaruwa dataimakon Shaiɗan, Attishawa kuma tana
faruwa saboda karanta abunci, kuma jiki yakan samu nishadi da karsashi saboda
dataimakon Allah take samuwa,.
Imamun
Nawawi rahimahulla ya ce: An danganta hamma zuwa ga Shaiɗan ne, saboda yana
janyowa jiki sha'awa, kuma yana faruwa saboda jiki yai nauyi dacika shi da
abunci, abun nufi shi ne tsoratarwa daka abubuwan dasuke haifar da hammar, shi
ne cika ciki ta wajan ci ko sha.
Da Annabi
sallallahu Alaihi wasallam ya ce: Idan dayanku ya yi hamma yamar da ita
gwar-gwadon iyawarsa) ana nufin ya yi riko da abubuwan dasuke hana yinta, bawai
ana nufin mutum yahana zuwanta ba, domin idan tafaru ba a iya mayar da ita
ahakika, wasu sukace: (idan yai hamma) ana nufin idan yai nufin yin hamma.
Abun da ake
nufi da fadinsa a cikin hadisin muslim (Shaiɗan yana shiga) zai dauki ma'anar
shiga tahakika, saboda Shaiɗan yana gudana ajikin ɗan adam kamar yanda jini ke
wakana ajikinsa, saidai bashi dawani abu dazai iya yiwa mutum matukar yana
cikin ambaton Allah, wanda yai hamma ahalinda baya cikin ambaton Allah Shaiɗan
zai iya shiga bakinsa shiga ta hakika.
Zai iya ɗaukar
kuma an ambaci cewa Shaiɗan zai shiga bakinsa, ana nufin zai samu dama a kansa,
domin sha'anin abun da yashiga cikin wani shi ne yasamu dama a kansa.
Umarni
dacewa mutum yasanya hannu, ana nufin idan yai hammar ya sa hannu yarufe
bakinsa, da makamantansa.
Yana daka
cikin ma'anar sanya hannu abakinsa sanya tufafi da abun da zai iya zama manufar
da'akeso ta rufe baki, ana ayyana hannune idan babu abun da za a maida hammar
da shi babu banbanci tsakanin wanda yake sallah dawanda yake wajen sallah,
saidai umarnin zaifi karfi lokacin da mutum ke cikin sallah, hani da'akai kada
mai sallah ya sanya hannunsa abakinsa, anyi togaciya banda lokacinda ya yi hamma.
Yana daka abun da aka umarci mai sallah dayi
idan hamma ta zo masa yana cikin sallah, ya dena karatu, har sai yagama hammar
dan kada ya canja tsarin karatu.
Fat hu baari
(10/612).
Imamun
Nawawi rahimahullah ya ce: " idan mutum yai hamma a cikin sallah ko awajan
sallah mustahabbine yasanya hannunsa akan bakinsa, an karhantawa mai sallah
yasanya hannunsa abakinsa, idan ba hamma damaka mantantaa ya yi ba. Al'azkarr (346).
Saboda haka
hukuncin hamma asallah bawani abu bane, illah kawai duk lokacin da mutum zai
fara sallah, yafara da kwarin jiki da nishadi yasani Shaiɗan makiyinsane,
yadaukeshi amatsayin mikiyi, duk lokacin da hamma ta zo mai yai iyakacin
kokarinsa wajan maida ita, idan taci karfinsa ya sa hannunsa akan bakinsa.
Sannan ya
nisanci ababen dake haifar da hammar kamar cin abunci sosai da cika ciki da
abubuwa barkatai
WALLAHU A'ALAM.
سبحانك اللهم
لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.
Tambaya da
Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai
+2348123432272
+2348163731622.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.