Hukuncin Amfani Da Laya Da Guru

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalam Alaikum. Malam, mene ne hukuncin amfani da LAYA ko GURU a musulunci?

    Allah ya sa mu dace.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikum assalam, To ɗan'uwa Layu da guru sun kasu kashi biyu:

    1. Layun da aka yi su da Sakandami ko Hatimi ko sunayan aljanu ko wani abu na daban wanda ba Alkur'ani ba, wannnan malamai sun cimma daidaito game da haramcinsu kamar yadda ya zo a Fataawaa Allajna Adda'imah 2/212 saboda faɗin Annabi ﷺ (LAYU da kuma abin da ake daurawa mace don miji ya sota shirka ne) kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (3883) kuma Albani ya inganta shi, sannan da hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito mai lamba ta: (16969), inda Annabi ﷺ yake cewa: (Wanda ya rataya laya to ya yi shirka, shima wannnan hadisin Albani ya inganta shi a Silsila Sahiha.

    Hadisan da suka gabata suna nuna haramcin daura Laya saboda Manzon tsira ya kira ta da shirka, shirka kuma tana fitar da mutum daga musulunci.

    2. LAYUN da aka yi su daga Alƙur'ani ko hadisai ingantattu, waɗannan na'u'i malamai sun yi saɓani a kansu:

    i. Sun halatta saboda sun kunshi sunan Allah da kuma karatun alƙur'ani wanda sifar Allah ce, wanda ya dogara da su ya dogara ga Allah, wannan ita ce maganar Amru bn Al-ass da Aisha da wasu daga cikin magabata.

    ii. Ba su halatta ba saboda ba a samu Annabi ﷺ ya yi ba, da hakan shari'a ne da an gan shi ya yi ko da sau ɗaya ne a rayuwarshi, sannan rataya layun da suke dauke da Alƙur'ani zai jawo a wula kanta su tun da za a shiga wurare marasa tsarki da su lokacin biyan bukata, kiyaye hakan kuma yana da kamar wuya.

    Zance mafi inganci shi ne haramcin amfani da Layun da suke daga Alƙur'ani saboda dukkan alkairi yana cikin biyayya ga Manzon Allah ﷺ sannan shari'ar musulunci ta halatta mana addu'o'i da yawa na neman kariya waɗanda suka wadatar da mu daga layu.

    Don neman karin bayani duba: Taisirul Azizil Hamid shafi na: (136) da kuma Ma'arijul Kabul 2/510

    Allah ne mafi sani.

    Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

    𝐅𝐀𝐂��𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.