Ticker

HUKUNCIN AUREN ‘YAR ZINA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Dan Allah yaya matsayin auren macen da aka haifa ba ta hanyar aure ba, Amma ansan iyayen nata?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa’alaykumussalam.

Da farko dai mu sani cewa ita yar zina ba ta da laifi tana da duk wani hakki na yar aure..

Na biyu: Malamai sun yi saɓani wajen jingina ɗa/yar zina zuwa ga waɗanda suka samar da ita (iyayen da suka yi zinar).. Jamhurun malamai sun tafi akan cewa baza’a jin gina ta zuwa ga mahaifin ba sai dai mahaifiyar, amma fatawar da aka nakalto daga Hassanul basari da ibnu sireen da urwa da ibrahim annakha’i da ishaaƙ da suleiman ibn yassaar cewa za’a jingina ta ga mahaifin kuma shaihul islam ibnu taimiyya ya zaɓi wannan zancen..

Don karin bayani aduba:

Fatawal kubura 3\178 da Al’furi’u 6\625 da Al’ Mugny 9\122.

Na uku: malaman da suka kore jingina ta ga mahaifin ta sunce batada waliyyi don haka waliyyin shi ne hakimi wato sun yi hujja da hadisin abu dauda 2083

Waɗanda kuma suka tabbatar da jingina ta ga mahaifinta sunce shi ne waliyyin ta.

Aduba: asannal madaalibi 13\288 da Al’iƙnaa’u 4\505

Wallahu A’alam.

Malam:Nuruddeen Muhammad (Mujaheed).

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments