Hukuncin Bacci Bayan Sallar La'asar

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Wanne Hadisi Ne Ya Hana Bacci Bayan Sallar La'asar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله العلي العظيم.

Babu wani hadisi daya inganta dangane da bacci bayan Sallar la'asar, na yabo kona zargi,.

Daka cikin Hadisan ƙarya waɗanda suka shahara abakunan mutane akan bacci bayan sallar la'asar akwai hadisin dake cewa: (Wanda yai bacci bayan la'asar, sai hakanlinsa ya gushe, ya zama mahaukaci , kada ya zargi kowa sai kansa.)

Albani a cikin Sil-sika za'iyfah mujalladi na daya shafi na 112) hadisi na (39) ya ce:

 Hadisin Mai raunine, Ibnu hibbaan ya ruwaito shi a cikin littafinsa " Azzu'afa'u wal-majruheen (1/283) ta hanyar khalid bin Ƙasim daka lais bin Sa'ad daka aƙeel daka zuhry daka Urwa daka Aisha.

Ibnul jauzy ya ruwaitoahi a cikin " Al-Mauzhu'ãat (3/69) ya ce: Bai inganta ba, khalid maƙarya cine, hadisin ibnu luhaiƙa ne sai khalid ya daukeshi ya jinginawa laith, .

Menene Hukuncin Bacci bayan Sallar la'asar?

Malamai Sunada zantuka guda biyu akai.

1. Zance na farko malaman fiƙhu sukace: Makaruhine suna dogaro da wancan hadisi mai rauni daya gabata

2. Zance na biyu kuma Sukace: makaruhine amma suna dogaro da wasu magan-ganun magabata, da kuma Abun da ilmin likitancin musulunci ya tabbatar.

Yazo daka kawwaat bin jubair ɗaya daka cikin sahabbai ya ce: Bacci bayan la'asar haukane da dabbanci.

Yazo daka Makhuul cikin tabi'ai yana karhanta yin bacci bayan la'asar, yana jiyewa mai yinsa kada ya kamu da cutar wasi-wasi.

Duba Musannaf na ibnu Abiy shaybah (5/339).

Maruzy ya ce: Naji Imamu Ahmad yana cewa: yana jiyewa mutumin da yake bacci bayan la'asar tabuwar hankalinsa.

Ibnu muflih ya ciro wannan a cikin "Aãdabul shari'ah (3/159) da ibnu abiy ya'alah a cikin Dabaƙatul Hanabila (1/22).

Ibnul Ƙayyeem a cikin zhadul ma'ad (4/219) ya ce:

Baccin rana bashi da kyau yana haifar da cututtuka na dafewar jiki dana musiba idan ta sauka, yana bata launin jiki, yana haifar da cutar hanta, yana raunana kashin gadan baya, yaka raunana sha'awa, sai in alokacin zafine. Maganinsa bacci bayan la'asar.

Abdullahi dan Abbas yaga ɗansa yana bacci da safe yace dashi, tashi kana bacci alokacin da ake raba arziƙi?.

Wasu magabata Sukace: Wanda yai bacci bayan la'asar hankalinsa ya hargitse kada yazargi kowa saidai kansa.

Duba Madalibu Ulinnahyi (1/62) da Giza'ul Al-baab (2/358) da kashshaful Ƙina'i (1/79) da Adabul Shari'a na Ibnu muflih (3/159) da Adabul dunya waddeen (355-356) da Sharhin Ma'anil Ãaasaar (1/99).

Gaskiyar Magana Ita ce: BACCI BAYAN LA'ASAR YA HALATTA domin asali shi ne halacci, ba a ruwaito wani hadisi ingantacce daya hana ba, Hukunce-hukuncen shari'a ana daukarsu ne daka hadisai ingantattu, bawai daka hadisai masu rauni ba, balle hadisan ƙarya, ba kuma adauka daka ra'ayoyin mutane.

Yazo afatawa lajnatul da'imah: Bacci bayan sallar lar'asar babu laifi a kansa, wannan magana ita ce mai rinjaye, abun da ya zo daka wasu salaf magabata nakwarai ana dorashi akan karhanci ta fuskar likitanci, bawai tafuskar shari'a ba, ya shahara tsakanin larabawa ada can da wasu likitocin da can bacci bayan la'asar ba lafiya bane, yana iya kaiwa ga cutarwa ajiki, sai ake hana mutum ya yi bacci bayan la'asar dan kada ya cutar da kansa, ba tare da jigina hakan zuwa shari'a ba, yana komawa zuwa ga likitanci, idan ya tabbata ta bangaren wanda yake baccin cewa yana cutar dashi, sai ahana mutum, dan kada ya cutar da kansa, amma ashari'a hani bai ingantaba tun farko.

Fatawa lajnatul da'imah (26/148).

Wallahu A'alamu.

🖊 Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments