𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, menene hukuncin namiji mai duka, har ya sumar da matansa, wani lokaci har ya yi mata targade, shin ya halasta a zauna da irin waɗannan mazan, domin dukan mace shi ke sanya wasu matan su nemi hanyar kare kansu, idan da tsautsayi har a rasa rai. Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salamu, duk lokacin da mace ta saɓa wa mijinta a harkar zamantakewar aure, to
Shari'a ta ba da bayanin matakai da ya kamata a bi don ganin an yi wa mata
gyara, idan muka koma Alƙur'ani mai girma za mu ga inda Allah Maɗaukakin Sarki
ke cewa:
"Matayen da kuke tsoron saɓawarsu, to ku yi masu wa'azi, ku ƙaurace masu a shimfa, ku dake su, amma idan suka yi maku biyayya kada ku nemi hanyar cutar da su, lallai Allah Ya kasance Mai ɗaukaka ne Mai girma. Suratun Nisá'i aya ta 34.
Malaman Tafsiri sun nuna cewa waɗannan matakai guda uku su ne miji zai bi wurin mu'amala da matarsa a lokacin da ta saɓa wa umurninsa ko umurnin Allah, wato da farko zai fara yi mata wa'azi da nasihohi ne, ba sau ɗaya ba, a lokuta mabambanta, idan ba ta gyara ba sai ya ƙaurace mata a shimfiɗa, wato ya daina kwanciya da ita, idan duk ta ƙi gyara halinta bayan waɗannan matakai guda biyu, to yana iya dukanta amma ba duka mai cutarwa ba, kamar yadda malamai suka bayyana a Tafsirai. Amma wasu malaman sun ce barin dukan ya fi, duk da kasancewar addini ya ba da damar a yi.
To a nan ne ake samun wasu mazajen da ba su san abin da suke yi ba, idan suka zo dukan matayen nasu sai su yi masu dukan mahaukata, har a ji ma wata rauni, to ba haka ayar take nufi ba, irin dukan da ake nufi shi ne duka ba mai cutarwa ba, duka ba mai cutarwa ba kuwa shi ne dukan da idan aka yi shi ba zai nuna alamar duka ba, kamar yadda malamai suka bayyana, kuma barin dukan ya fi alheri, amma fa ya halasta a Musulunci bayan an bi matakin nasiha da ƙauracewa shimfiɗa duk abu ya ƙi gyaruwa kamar yadda ayar Alƙur'ani ta nuna.
Saboda haka ba dai-dai ba ne a bayar da aure ga wanda aka san yana sumar da matarsa ba, ko wanda yake dukan matarsa har sai ta yi targaɗe ko makamancin haka ba, saboda duka ba mai cutarwa ba aka ce, idan kuma ita mace ta ga za ta iya zama da irin wannan miji ganin damarta ne ba za mu hana ta ba. Kuma lallai mata ya kamata su ma su sani lallai maganar dukan nan addini ya aminta da shi amma fa ba mai cutarwa ba, saboda haka, masu kore dukan kwata-kwata su ce Musulunci bai zo da shi ba kuskure ne, sai dai barin dukan ya fi alheri.
Domin neman ƙarin bayani a duba TAFSIRU RAÁZIY, wato MAFAÁTEEHUL GAIB a ƙarƙashin aya ta 34 na SURATUN NISÁ'I.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Tambaya
Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za ku iya
bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.