Hukuncin Halartar Bikin Kirista

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin ya halatta musulmi yahalarci bikin kirista a coci?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله

    Shiga cikin Coci Asali Halal ne, haka yiwa kafiri barka a munasaba keɓantacciya aduniyance data shafeshi halal ne, kamar yi masa barka dayin Aure, ko Samun wata Nasara akan wani Abu, jarabawa Samun Aiki ko samun Haihuwa.

    Hukuncin shiga coci halal ne awajan mafi yawan Malamai, batare da karhanci ba, Duba Al'insaaf (1/496).

    Wasu Sukace: Ya halatta ashiga coci idan Babu hotuna acikinta ko gumaka agirke acikinta.

    Sahihiyar Magana Ya halatta shiga coci koda akwai hoto acikinta, inwani dalili yasa ashiga ɗin.

    Duba: Bukhary (1276) da Almusannaf (4871) da Ahkamu Ahlul Zimmah (3/164), da Al-Musannaf Na Abdurrazaƙ ( 1610) da Al-mugny (8/113).

    Halayen dabai Halatta musulmi yaziyarci Coci ba, ko Wajan Bautar kafirai ba.

    1- Lokacin dayake da Munasaba da Wani idi Nasu, ko wata Munasaba tasu ta Addini, ziyartar coci awannan halin yazama tarayya dasu acikin idinsu nakafirci wanda Shari'ah ta hana.

    Umar Allah yaƙara yarda dashi ya ce: Kada kushiga cocin kafirai lokacin bukukuwansu domin fushin Allah yana sauka akansu.

    Musannaf Na Abdurrazaƙ (1609).

    2- Idan yazama za'a lazimtawa wanda suke acocin suyi tarayya wajan wani Abu na addinisu, kamar Anemi wanda yaje cocin yagabatar ko Aikata wani Abu dayake akwai girmamawa ga Abun bautarsu kamar durkusawa ko sunkuyar da baya ko tsugunawa ko rankwasar da kai, ko wake

    3-Idan Mai zuwa Coci yana tsoran fitina akansa, kada wani Abu yasameshi, to jefa masa rudu azuciyarsa cikin Abunda zai gani koya ji, wannan yana sa wanda baida ilmi da wayau lalacewar Addininsa.

    4- Idan Bada izininsune ba, ko kuma Zasu Dauki zuwanka kamar izgilancine da Addininsu da ibadarsu.

    5-Idan Akwai wani Al'amari dazaisa ka fitinu saboda shi, wanda wannan zaisa wanda baida ilmi ya dauka kamar kana tabbatar da Abunda sukene, kamar yanda yake aƙissar Umar dan Khaddab Allah yaƙara yarda dashi.

    6-Idan zuwanka zai zama awata sifa ta tabbatar da Abunda suke fadi da aikatawane na kafirci da Shirka acikin sallar su da ibadarsu.

    Hukuncin Ziyartar biki a Coci

    Bikin Aure idan ba bikine Na addininsu ba, kuma yakubuta daka Ababen dasuke haramun kuma yakubuta daka Ababen da'aka hana ziyartar coci acikinsu, kuma bai hadu da Al'ada ta tsiraici da ketare iyaka da munanen Halaye wanda zai gudana daka mahalarta ko Amare ba, inkaga akwai Maslaha kana iya halarta, inhar babu Abu daya da shari'a ta tsoratar awajan..

    Domin Yana cikin asalin halaccin zuwa coci amunasaba ta harkar duniya.

    Mussaman idan Akwai alaƙa ta zuwa kamar kiransa zuwaga addini.

    Dan haka Bai halatta kaje bikin Auren Abokinka kirista ba koda ba'a coci bane, indai bikin yana da alaƙa da wani abu dasuke ƙudurcewa acikin addininsu, ko akwai abunda shari'a ta tsoratar akansa.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za ku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.