Ticker

Hukuncin Kwanciyar Ruf-Da-Ciki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam. Dan Allah ina da tambaya ce. Dan Allah wai da gaske ne duk mai kwanciya bacci ya kifa ciki babu kyau, sai a ce dan wuta ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa’alaikumus Salam, Abin da malamai suke cewa shi ne; kwanciyar ruf-da-ciki makaruhi ne saboda an ruwaito daga Manzon Allah ﷺ cewa, ya ga wani mutum daga cikin Sahabbansa a kwance ya yi ruf-da-ciki, sai ya zungure shi da ƙafarsa, ya ce: "Lallai irin wannan kwanciyar Allah Mai girma da buwaya yana ƙyamar ta".

Hadisi ne Hasanul Ligairihi, kuma Abu Dáwud ya ruwaito shi a lamba ta 5040.

Saboda haka kwanciyar ruf-da-ciki abin ƙyama ne, ba a son mutum ya yi ta sai idan akwai lallurar da ta sa buƙatar hakan. Duk da haka kuma bai dace a ce ma wanda aka ga ya yi kwanciyar ruf-da-ciki ɗan wuta ba, duk da kasancewar kuwa akwai wata ruwayar hadisi mai rauni da aka ce Annabi ﷺ ya ce: "Kwanciya ce irin ta ‘yan wuta", to ko da ma a ƙaddara wannan magana ta inganta, to ba ta nuna cewa a kira wanda ya yi kwanciyar ruf-da-ciki ɗan wuta, sai dai a ce ma wanda ya yi hakan ya yi makaruhi.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments