Hukuncin macen da take tona asirin mijinta

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Macen Da Take Tona Asirin Mijinta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله الذي خلق كل شي ء أزواجا.

Shari'a ta yi Hani Akan Ma'aurata sudunga Bayyana sirrin dake Tsakaninsu musamman na Mu'amalar Aure.

Hadisi ya Inganta daka Abu Sa'idul khudry Allah yaƙara yarda dashi ya ce: Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce: (Mafi Sharrin Mutane ranar Alƙiyama Awajan Allah shi ne Mutumin dazai kwanta da Matarsa, da Macen dazata kwanta da Mijinta, Sannan suje su yaɗa sirrin junansu ) Muslim (1437).

Imamun Nawawi Allah Ya jiƙansa da Rahma Ya ce: a cikin Hadisin akwai haramcin Namiji ya yaɗa abun da ya gudana shida Matarsa na Al'amuran jin daɗin sha'awa, Ko siffanta wannan jin daɗi, Ko Wani Abu daya gudana Tsakaninsa da Matarsa na Zance ko aiki da makamantansu wanda ya shafi sirrin jin daɗin Aure tsakaninsu..

Sharhin Muslim (9 /10 ).

Saidai Idan Buƙatace ta kama na Bayanin Wani hukunci shari'a ko Saboda a yi Masa Nasiha ko don kore Wata husuma dake tsakanin Ma'aurata Babu laifi don mace ko miji ya fadi wani Abu na Matarsa, Indai don irin wadancan Manufofinne Nagyara da dawo da Mutum zuwaga dai-dai Hakan Babu laifi.

Amma Duk da Hakanma Ba'ason Miji ko Mata tafito Ƙarar tafadi wani sirrin mijinta koya faɗi na Matarsa, ko da da Manufar gyarane ko neman wani hukunci Na shari'a, idan za a iya sayen Maganar afahimta, shi akafiso Akan ta fito falo falo ta fada.

Hadisin Aisha Allah Yaƙara yarda da ita ya Nuna haka ta ce: (Wani mutum Ya Tambayi Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam Yana jima'i da matarsa sai ya gaji, Shin akwai wanka a kansu, Aisha tana Zaune kusa da Annabi sai Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Muna yin haka nida Wannan, Sannan sai muyi Wanka ) Muslim (350 ).

A cikin Hadisin Akwai Halacci Ambaton irin hakan agaban matarka idan akwai maslahar yin hakan, kuma Babu wata cutarwa dazata auku, Annabi Yafadi haka ne da Waccan siga don yafi darsuwa azuciyarsa.

Sharhin Muslim (4/ 42 ).

Badai-dai Bane don daɗin Baki da tsugudidi Mace ko Miji yaje yadunga fadawa Abokansa sirrin dake tsakanisa da matarsa, Yin hakan yana cikin manyan Laifuka kuma Haramun ne, Saifa Abun da buƙata takai dasai An bayyana don Bayanin Wani hukunci Na shari'a , ko Wata maslahar shari'a .

WALLAHU A'ALAMU.

Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Nakwarai.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments