𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum dan Allah malam laifi ne dan mijin mace ya ɓata mata rai ta yi yaji ta
ƙaurace masa a wajen shimfida?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam,
'Yar uwa a gaskiya abin da shari'a ta nuna shi ne bai halasta mace ta ƙaurace
wa mijinta a shimfiɗa ba ko da ya ɓata mata rai matuƙar ya kiyaye haƙƙoƙinta da
Allah ya wajabta masa, saboda hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah Allah ya ƙara
masa yarda ya ce:
Manzon Allah
ﷺ ya ce:
"Idan
namiji ya kira matarsa zuwa shimfiɗarsa sai ta ƙi, har ya kwana yana fushi da
ita, to Mala'iku za su yi ta tsine mata har wayewar gari".
Bukhariy
(3237), Muslim (1436).
Saboda haka,
lallai mata su guji ƙaurace wa mazajensu a lokacin da suka buƙace su, saboda
kauce ma wannan tsinuwa na Mala'iku, su kuma mazaje su ji tsoron Allah su daina
ƙuntata wa matayensu.
Abubuwan da
suke zama uzuri ga macen da mijinta ya neme ta ta ƙi su ne, kamar mace tana
jinin haila, ko jinin biƙi, ko rashin lafiyar da idan ta yi jima'i za ta cutu,
ko abin da ya yi kama da haka na uzuri karɓaɓɓe a Shari'a, sai dai shi jinin
haila da na biƙi ɗin suna hana saduwa ne, amma ba sa hana jin daɗi daga abin da
ke saman gyauto.
Allah S.W.T
ne mafi sani.
Jamilu
Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.