𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin Ya
Halatta Mace Ta Dunga Rage Kuɗin Cefane Da Mijinta Yake Bata Tana Bukatunta
Dasu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
Idan miji
baya ciyar da matarsa da 'ya'yanta ciyarwa tawajibi, ya halatta tadunga diban abun
da zai ishesu suci su sha ita da 'ya'yanta ba tare da ɓarna ko wuce gona da iri
ba, ba tare dasanin mijinba, saboda hadisin A'isha Allah yakara mata yarda ta
ce: hindu bintu Ut-bah tace ya manzan Allah ﷺ lallai Abah sufyan mutum ne mai
makwo, baya bani abun da zai isheni nida 'ya'ayana sai abun da nake ɗauka daka
dukiyarsa ba tare da saninsa ba, sai ya ce: (kiringa ɗaukar abun da zai isheki
da 'ya'yanki da kyautatawa ba tare da ya sani ba). Bukhari (5364).
Shaukani
rahimahullah ya ce: A cikin hadisin Akwai dalilin dake nuna wajibi ne miji
yaciyar damatarsa, haka kuma akwai wajabcin Uba dole ne yaciyar da ɗansa, malamai
sun yi ijma'i akan hakan.
Haka duk
wanda ciyar damutum yake wajibi a kansa yahalatta wanda ake ciyarwar yadunga
tsakurar abun da zai isheshi idan wanda keciyar dashi ɗin baya kamantawa, kuma
yanaci gaba dayi masa kwauro, Nailul Audaar (6/383).
Haka kayan
gyaran gida kona shimfida dana cin abunci dana kwanciya bacci da tufafi
yahalatta mace tadau kuɗin mijinta ba tare da ya sani ba ta siya inyaki yimata
ko baya mata ba tare da sanin sa ba, duka wajibi ne a kansa yasamar dasu ga
matarsa da 'ya'yansa.
Ibnu ƙudama
rahimahullahu ya ce: wajibi ne miji yasamarwa matarsa abun da zata bukata
nashimfida tai bacci, kama daka katifa, bargo, gado, mayafi, filo, gaba daya
zai samar mata gwar-gwadon yanda al'adar garinsu tagudana akai sune mace take
amfani dasu wajan kwanciya, da abun da zatake zama da rana natabarma yanda aka
saba agarinsu shi ne akasan matar aure tana tanadarsu, da darjumar sallah,
tabarmar tsakar daki ko kafet, mai kudi komai arziki dai-dai arzikin miji ko
samunsa, talaƙa zai yi shima dai-dai matsayinsa batakurawa akai kowa dai-dai
samunsa da arzikinda Allah yahore masa. Al-Mugni (8/169).
Amma indai
ba irin wannan bane damukai bayani haramun ne mace tarage kuɗin cefane tana
wasu bukatunta, sai ta tambayeshi yabata nasauran bakatunki wanda suma kinada haƙƙin
yabaki kuɗi kiyisu indai basufi karfinsaba ko kuma basu da wani tasirinda zaki
damu kanki.
Hakan yana
cikin cin amana da ha'inci wanda haramnne amusulunci baya daka cikin dabi'u na
mutanen kirki.
Saidai akwai
mazan dasuke bayarda kuɗin cefanen dasunsan yafi karfin cefanen daza'ayi suna
bayarwane dama daniyyar abun da yaragu kiriƙe kiyi amfanin kanki dasu, wannan
baza'ace haramun bane bal-ma yana daka cikin kyautatawa.
Da irin
wannan ne wasu masu tausayi dahankali daka cikinku suke adashi da kuɗin dan
lokacin da aka samu tasgaro ko matsalar abun yauda kullum sai wadannan kuɗaɗe
da miji kebayarwa suyi masa rana kuma kikara ƙima da daraja azuciyarsa yakara
nutsuwa dake soyayyarki takaru a cikin zuciyarsa.
Kawai abun
da zakiyi shi ne kizaunar dashi cikin hikima da zolaya da fira tajan hankali
kibugi cikinsa ki nuna masa kuɗin cefanenda yake baki shin yana sane dacewar
sunfi karfin cefanenku atsaka tsakiyar cefanen daya kamata kuyi, wanda babu ɓarna
a cikinsa, ko barnatar da dukiya, inyana sane kin ga kin san matsayin abun da
kike ragewar halalne tsantsa, inkuma kawai yana bayarawane anufinsa shi ne abun
da zai isheku saiki nunar masa cikin hikima dawayo cewa anya baya yawa kuwa ko
kuma ya yi yawa, saiki nunar masa wani lokacin kina ragewa kina danyin wasu
harkokinki inya amince koyaci gaba dabaki yanda yasaba koya kara duk baki da
matsala dankin rage.
Amma haka
siddan baki fahimci mijinki yana bakine acewar yana sane sunfi karfin cefanenku
kawai danki rike sauran yake bakiba, kidunga rage wani abu kina bukatunki, babu
shakka wannan kus-kurene babba wanda duk randa yagano zai iya haifar muku da
mummunar matsala tsakaninku.
Allah maɗaukakin
sarki yatsaremu daka shawara da kuduba irinta Shaiɗanun aljanu da mutane.
WALLAHU
A'ALAM
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.