Hukuncin Sakon Gaisuwar Juma'a (Jūma'at-Mubārak)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

A Shari'ance Mene ne hukuncin Sakon Gaisuwar Juma'a, da'ake ayiwa Mutane ta Text ko Social Media??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

​Ko shakka bābu cewa ​Rānar-Jūma'a​ rānāce ta īdi awajen Musulmai, kamar yadda ya zo a Hadīsi cewa ​Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ)​ Yāce:​

​إن هذا يوم عيد جعله الله للمسلمين، فمن جاء إلي المسجد فليغتسل.......... (رواه إبن ماجه/1098)​

​​MA'ANA​​

​​Lallai wannan rānāce (Jūma'a) da Aʟʟāн(ﷻ) ya sanyāta amatsayin īdi ga Musulmai, danhaka idan Mutum zaije Masallāci to ya yi wanka,......​​

​Dan haka kenan Musulmai sunada ​rānekun īdi​ ne guda uku kawai a Muslunci,​

​​-Īdin-Rānar-Jūma'a:​​

​​-Īdin-Babbar-Sallāh:​​

​​-Īdin-ƙaramar-Sallāh:​​

​Saidai ​Īdin-Babbar-Sallāh da Īdin-ƙaramar-Sallāh​ sukan maimaitune aduk Shēkara, amma ​Īdin-Rānar-Jūma'a​ yakan maimaitune duk ​Sāti-Sāti,​​

​Amma dangane da abinda yashāfi hukuncin ​Sakonu-Gaisuwar-Jūma'a,​ da Mutāne sukeyi atsakaninsu, kamar irin su:​

​​Jūma'at-Karīm,​​

​​Jūma'at-Mufīdat,​​

​​Jūma'at-Mubārak,​​

​​Jūma'at-Ɗayyibat,​​

​Dadai sauran makamansu, sai ariƙa aikāwa 'Yan'uwā da abokan arziƙi ta hanyar ​Text-Message,​ kokuma ta ​Social Network,​ Abinda yake a ​Shari'ance​ kamar yadda ​Mālamai​ suka faɗa shi ne, Asali Muslunci yā yardane kawai da ​Gaisuwar Rānekun Īdin-ƙaramar-Sallāh da Babbar-Sallāh,​ sūmā abisa ga wasu lafuzza da ​Shari'a​ ta yarda a yi amfāni dasu, amma gameda ​Gaisuwar-Jūma'a,​ bābu inda ​Shari'a​ ta yi bayānin cewa ayi, danhaka dayawa daga cikin ​Mālamai​ sukace yin ​Gaisuwar-Jūma'a Bid'ace,​ musamman idan yakasance māsu yin hakan suna ƙudurta cewa akwai wani lada da za a sāmu ga duk wanda yayi, to ko Shakka bābu cewa yā zama ​Bid'a,​ domin ba'asamu hukuncin yin hakan a cikin wani ​Nassi​ ko aikin magabāta ba,​

​Saidai akwai ​Mālaman​ dasuke ganin cewa idan Mutum ya yi ​Gaisuwar-Jūma'a,​ tare da cewa yāsan bāta da asali a cikin addīni sannan kuma bai ƙudurta cewa yin hakan Sunna bane, kokuma idan Mutum yāyi zai sāmu wani lādā akaiba, kawai suna yine amatsayin ​al'āda​ bawai da sunan addīniba, sukace to bābu wani laifi a kansu dan sunyi, saidai duk dahaka sukace barin yinsa ɗin shīne yafi zamā alkhairi, saboda gudu kada ​Jāhilai su rūɗu​ da cewa hakan ​adiīnine,​ wanda kuma gālibin māsu aika ​Sakon-Gaisuwar-Jūma'a,​ awannan zāmanin zāka sāmu cewa suna yīne danufin sāmun lādā bawai suna yine amatsayin al'ādaba, ​Aʟʟāн(ﷻ)​ dai Ya gānar damu gaskiya kuma yabāmu īkon binta ​Āmīn-Yā-Rabbi,​​

Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:​​

 ​​↓↓↓​​

​"زاد المعاد" (1/380)​

​"الفتاوي الكبري" (2/228)​

​​шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'αʟαмυ

 ​​AMSAWA

 ​Mυѕтαρнα Uѕмαn​

 ​08032531505​

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments