𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum. Tambaya malam
saurayi da budurwane shaiɗan yashiga tsakaninsu har yakaiga saurayin ya tsotsi
nonon budurwan har saida ruwa ya fito. Hakan yafaru ba so ɗaya ba, ba biyu ba
amma ba ta taɓa ganin ruwan ba sai ranar. To mallam yaya hukuncin aurensu, ya
halatta suyi auren? Kuma minene hukuncin shan Ruwan da yayi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa’alaykumussalam, To ɗan’uwa
wannan abin da suka aikata mummuna ne, Tun da Allah ya haramta taɓa jikin matar
da ba ka aura ba, kuma kofa ce da za ta kai zuwa zina, idan mutum ya tsotsi
nonon mace bayan ya girma Amma babu ruwa a ciki, wannan ba zai haramta musu
aure ba, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi saɓanin akan hakan zuwa
maganganu guda biyu :
1. Ya halatta su angunce, saboda
kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika
shakaru biyu, saboda faɗin Annabi ﷺ “Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce
yaro ya sha saboda yunwa” , Bukhari lamba ta : 5102,
Ma’ana lokacin da ba zai iya
wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne
bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan
ita ce maganar mafi yawan malamai.
2. Yana haramta aure, saboda ko da
yaushe mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi ﷺ ya
umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta agare shi, kamar
yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin
Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai
yi tasiri wajan haramcin aure.
Zancen da ya fi karfi shi ne nonon
da mutum ya sha bayan ya girma ba ya haramta aure a tsakaninsa da matar da ta
ba shi.
Don neman Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid
2\67.
Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah,
tabbas zai kiyaye shi, Wanda ya saɓa masa zai same shi a madakata.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu zarewa
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za
ku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.