Ticker

HUKUNCIN SAYAR DA MAGANIN KARFIN MAZA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam mutum ne yana da chemist yana sayar da magunguna. Ya halatta ya sayar da maganin karfin maza ga wanda yake so ya biya bukatar iyalinsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, In har an jarraba an samu yana amfani kuma likitoci sun tabbatar ba ya cutarwa ya halatta a siyar da shi don aure ya gyaru, a kara samun donkon soyayya, saboda saduwa tsakanin ma’aurata turke ne tsayayye, wanda in ya goce aure ba zai tafi saiti ba, yana daga cikin ka’idojin Sharia duk harkokin mutane na yau da kullum waɗanda ba ibada ba ne sun halatta, in har ba’a samu nassin da ya hana ba.

Addinin musuluci ya haramta duk abin da yake cutarwa, kamar yadda nassoshi masu ɗinbin yawa suka tabbatar, wannan yasa duk maganin da likitanci ya tabbatar cutarsa ta fi amfaninsa yawa ya wajaba a guje shi, Tunkude cuta ginshike ne a cikin addinin musulunci.

Allah ne mafi sani.

Amsawa

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments