HUKUNCIN TSINTUWA

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Wani bawan Allah ne ya tsinci Naira: ₦500, a wurin kuma bai ga wadanda zai yi wa cikiya ba… Ya ya kamata ya yi da kudin tsintuwar?, suna ajiye yanzu haka kusan wata ɗaya.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    To dan’uwa idan mutum ya yi tsintuwa ya wajaba a gare shi ya yi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma in mai ita ya zo daga baya zai biya shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 5761.

    Amma idan  abin da ya tsinta dan kaɗan ne ba shi da yawa, to ya halatta ya yi amfani da shi ko da bai yi cigiya ba, saboda abin da aka rawaito cewa: Annabi ﷺ ya ga wani dabino akan hanya, sai ya ce: In ban da ına tsoron na sadaka ne da na ci. Muslim ya rawaito a lamba ta: 2527, sai hadişin ya nuna dan karamin abu ba ya bukatar cigiya.

    Malamai şun yi saɓani wajan iyakance tsintuwar da ba ta bukatar cigiya, wasu sun ce za’a koma al’adar mutane, duk abin da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to in an tsince shi ba ya bukatar cigiya, Ibnu Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa: bai wajaba mutum ya yi cigiyar abin da bai Kai a yanke hannu saboda shi ba, wato ɗaya bisa huɗun dinari, haka nan sayyadina Aliyu ya tsinci dinare ɗaya ya yi amfani da ita ba tare da ya yi cigiya ba.

    Abin da ya gabata yana nuna cewa: mutukar ba ka samu mai (₦5,00) ɗin da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta ka yi amfani da ita ba tare da cigiya ba, tun ba kuɗi ne mai yawa ba, kuma mai ita ba zai kwallafa rai Akanta ba.

    Don neman karin bayani duba: Al-mugni 6/351.

    Allah ne mafi Sani.

    Jamilu Yusuf Zarewa

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

     

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    [9:13 am, 17/06/2023] Malam Khamis Yusuf Tambayoyi: 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    idan farcen mutum ya karye ko gashinsa yana cutar dashi kuma ya yi niyyar layyah, yaya Zaiyi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wanda farcensa yakarye ko gashinsa yana cutar dashi yahalatta kawar dashi babu komai akansa, Ba'a daukarsa wanda ya aikata abunda aka hana wanda yai niyyar yin layya ya aikatasu, saboda kiyaye bukata dakawar da cuta, Wannan yana cikin saukakawa ta Allah madaukakin sarki.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.