Hukuncin Uban Da Yaƙi Aurar Da ‘Yarsa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene Hukuncin Uban Da Yaƙi Aurar Da 'Yarsa Bayan Tana Da Shekara 30?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

    Abun da ya kamata ga Uba shi ne ya godewa Allah da ya sa yarinsa takai matsayin Aure, ya yi gaggawar Aurar da Ita dan kwatanta Umarnin Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam da ya ce: (Yaku Taron Samari wanda ya Samu damar Aure a cikin ku to ya yi Auren, wanda bashi da dama ya dunga azumi, domin Azumi kariyane a gare shi.

    Bukhari (5065) da Muslim (1400).

    Wannan yashafi uban da Allah ya bashi diya wajibi ne Ya Aurar da ita da zarar takai munzalin Aure, dogaro da Umarnin Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam.

    Idan Kuwa bai Aurar da itaba, Saboda Wata manufa tasa tason duniya da buri da rudun Shaiɗan, ya tabbatar yana ɗaukar zunubin cutar da ita da yakeyi, sannan inta kasa haƙuri tana wasu ababe dan ragewa kanta sha'awa, kota fada zina lallai yana da Zunubi mai girma a kansa.

    Ya kamata ya hankalci wannan ni'ima da Allah yai masa na bashi diya harta kai matsayin Aure yana da ransa bai mutu ba, ya tuna cewa akwai wanda bai samu wannan ni'imar ba.

    Idan Saboda karatu yaƙi Aurar da ita, ya sani Karatu da Aure basa cin karo da juna, zai iyu a hadasu, ko da ta hanyar computer mace zatai karatun tana daka cikin gidan mijinta.

    Ga wata Nasiha da Shaik Abdul'azeez bin Baaz yai ga irin waɗannan jahilan iyayen.

    Ya ce: Wajibi ne Uba yai gaggawar Aurar da 'yah ko Ɗah Aure, bai dace ba Uba ya yi jinkirin Aurar da 'yarsa ko ɗansa saboda wai yana karatu, Aure baya hana komai na karatu, abune mai iyuwa ubah yaiwa 'yarsa Aure, tanaci gaba da kiyaye addininta da dabi'unta da kame ganinta, tare da haka tanaci gaba da karatunta.

    Koda zata fara karatunne daka baya takasa ƙarasawa saboda Auren babu laifi akai, muhimmin Abu shi ne ta koyi Abun da zatasan Addininta, Saura kuma cikwan kwalliya ne da wasu fa'idoji ba dole bane saitayi digree ko polytecnic ko N.c.e ko diploma, ko Samun Aiki ba.

    Aure Akwai Maslahohi masu yawa a cikinsa, musamman A wannan zamanin, Jinkirta yinsa kuma yana tattare da illoli da cuttuttuka masu yawa akan Namiji da Mace.

    Abun da yake wajibi akan iyaye shi ne gaggauta yiwa 'ya'ya Aure, idan budurwa ta samu Mijin da za suyi Auren.

    Majmu'u fatawa (20/421).

    Shaiek Usaimeen Ya ce: Hukuncin wanda zaiƙi Aurar da 'yarsa ko ɗansa saboda karatu koyace sai ta kammala makaranta kaza kosaita kai wasu adadin shekaru da maka mantan haka, Shi ne saɓawa Umarnin Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam (idan wanda kuka Gamsu da Halayensa da Addininsa ya zo neman Aurar 'yarku, toku Aurar masa)

    Turmuzi (1084)

     ya ce: Yaku Taron samari kuyi Aure domin yana sanya runtse gani yana sanya kiyaye farji..

    Abun da mukewa iyayen 'yan mata Nasiha shi ne kada mutum yaƙi Aurar da 'yarsa saboda bata gama karatu ba, ko wani dalili daban, ko koyarwa ko Samun Aiki, .

    Fatawa Ulama'u baladil haram shafi na (390).

    Ba Wani Abu bane idan Mijinta ya yarda zai barta taci gaba bayan sun yi Auren, ta ƙarasa karatun.

    Babu wata buƙata da zatasa ka dage akan dole sai 'yarka ta kammala karatun jami'a, indai ba wani ilmine kebantacce da'ake buƙatar mata suje su koya su ƙware akaiba saboda maslaha, kamar ilmin likitanci, matuƙar babu Wani Abu na haram a cikinsa.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.