Hukuncin Wanda Bai Riski Ruku'un Raka'a Ta Biyu Ba A Sallar Jumma'a

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Bansan Cewa Idan Mutum Baisamu Ruku'un Raka'a ta Biyu Ba a sallar juma'a Raka'a Huɗu Zai yiba, Nikuma Sai Nayi Biyu Yaya kenan?

    الحمد لله اللطيف الرحيم.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Babu Shakka duk wanda Bai riski ruku'un raka'a tabiyuba tare da liman asallar juma'a idan akayi sallama raka'a huɗu zai yi.

    Malamai sun yi saɓani akan cewa shin zai raka'a huɗu ne amatsayin Juma'a ko zai yita amatsayin Azahar ne kawai.

    Wasu sukace: zai yita raka'a huɗu amma zai niyyaci juma'a yake.

    Wasu sukace: zai yita raka'a huɗu amtsayin azahar kawai ba juma'a ba.

    Sahihiyar magana ita ce: zai yita amatsayin azahar ne juma'a takubuce masa, saboda fadar Annabi sallallahu Alaihi wasallam (Wanda yariski raka'a asallah hakika yariski jam'in sallah).

    Riskar raka'a kuma baya samuwa sai inka samu ruku'un raka'a ɗin.

    Dangane da raka'a biyu dakake abaya ba tare da sani ba

    Wannan babu komai akanka Allah baya kama mutum da laifin Abun da bai sani ba, ko abun da mutum ya aikata arashin sani ko hukuncin baikai gareshi ba.

    Saidai dawannan muke kara jan hankalin matasa akan wajabcin neman ilmin addini wanda zakasan hukunce hukuncen sallah wankan janaba wankan gawa abun da yashafi azumi zakkah hajji umara ziyara kisasi aure, dasauransu.

    Wajibi ne musulmi yasanya ilmin Sanin Addininsa sama dakowanne ilimi arayuwarsa.

    Raina musulunci ne kabar harkar kasuwarka ko ilmin rayuwa na neman abunci yahanaka neman ilimin addininka.

    Wajibi ne yanda kake hakura da abubuwan wal-wala ka jingine su gefe kai shekara biyar shida ka hakura da komai dandai kaga kasamu ilimin rayuwa na neman Abunci, to haka tilasne kaje ka kwashe shekara biyar shida kana zuwa makaranta danka samu abun da zakai addininka dashi, inma ba za ka makarantaba kabiya kuɗi akoya makaba, tilasne kasamu malami kadunga biyansa koya sanya maka lokaci kashekara biyar koshida kana koyan addini awajansa da ilmin dazai taimaka maka wajan samun wayewa ta addinin musulunci.

    Tilas kai haka inhar dagaske kake musuluncin za ka yi kuma dagaske aljannah kakesan samu dashi.

    Allah yaganar damu tafarki madai-daici.

    WALLAHU A'ALAMU.

    Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.