HUKUNCIN WANDA YA YI NIYYAN YIN LAYYA KUMA SAI YA FASA

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene hukuncin wanda ya yi niyyar yin layya kuma sai ya fasa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله

    Asalin layya sunnah ce mai ƙarfi, Alamace daka cikin Alamomin Musulunci na zahiri, Shari'a ta kwadaitar akanta ta bada muhimmanci akanta, Wasu malamai sun tafi akan wajabcinta ga wanda ya Samu dama.

    Idan Layya ta tabbata Sunnah ce, Wanda yai niyyar yi Saiya fasa babu komai akansa, Saidai idan ya riga ya ayyana dabbar da zai yanka ta hanyar cewa "Wannan layya tace" ko makamancin Haka abunda zai nuna ayyana layya, a irin haka dolene ya yanka layyar, bai halatta ya ce ya fasa ba, saboda ta fita daka mallakinsa ta hanyar ayyanawa.

    Idan ya sayo dabba da Niyyar layya bai ayyana ta ba da fadin " wannan layya tace" malamai sun yi saɓani, shin dole ya yanka ko A'a ?

    Abunda yake dai-dai bai zama dole ya yanka ta ba, kamar ya niyyaci bayar da gidansa waƙafi sannan daka baya ya fasa ba komai akansa, haka layya.

    Duba Al-Mugni (9/353) da Al-maj-mu'u (8/402) da Sharhin Mumti'i (7/466).

    Layya ba ta zama dole saboda niyya kawai,

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.