Hukuncin Wanda Yake Cewa Budurwasa Matarsa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene Hukuncin Mutum Ya Rinƙa Cewa Budurwarsa Matarsa Alhali Basuyi Aureba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله وحدة والصلاة والسلام على رسول الله.

    Yin hakan bai halattaba, irin waɗannan lafuzza wasane dawargi a cikin addini, Aure baya zama ingantacce saida waliyyin mace da shaidu, da sigar aure tsakanin mai neman aure da waliyyin mace, wali zaice: Na aurar maka da wance dayardarta, mai neman aure zaice nakarba, masu shaidawa su shaida sannan zata zama matarsa.

    Wajibi ne saurayi yadena cewa budurwarsa matarsa har sai yaje wajan iyayenta yanemi aurenta andaura musu aure tukun, sannn zai dunga kiranta da matarsa ashar'ance.

    Dan Kunsan juna kaɗai bai halatta yadunga kiran budurwarsa da matarsa ba, wajibi ne yaji tsoran Allah wajan yin alaƙa da budurwarsa

    Wannan bai hana Musulmi nagari yaso budurwa tagari, saidai mutum yadunga taka tsan-tsan wajen irin lafuzza daza su dinga ambatar juna da girmama junansu da nuna ƙauna tsakaninsu tare da gaggauta aure tsakaninsu.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.