Ticker

HUKUNCIN YIN AZUMIN NAFILA GA WANDA AKE BINSA BASHIN FARILLA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Shin ko ya halatta mutum ya yi azumin nafila alhali ana binsa bashin azumin farilla bai rama ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai sun yi saɓani dangane da hukuncin yin azumin nafila ga wanda a ke binsa bashin farilla, shin dole ne sai ya fara gabatar da ramuwar wannan farillar sannan ya ke da ikon yin nafila ko kuma a'a zai iya yin nafila daga bisani kuma ya yi farillar? An samu maganganun malamai kamar guda uku akan haka:

1. Ƙauli na farko shi ne, Mazhabin Hanafiyya da Zahiriyya sun tafi a kan cewa kai tsaye ba tare da wani karhanci ba ya halatta mutum ya yi azumin nafila kafin ya rama wanda a ke binsa na ramadan. Dalilinsu na cewa ya halatta shi ne, suka ce ba wajibi ba ne ga wanda a ke binsa bashin azumi a ce sai ya ramashi cikin gaggawa, dan haka yana iya jinkirta yin ramuwar azuminsa zuwa wani lokaci na gaba, sannan suka kafa hujja da wannan Hadisi na A'isha matar Mαnzoи Aʟʟαн(ﷺ) wanda take cewa:

"كان يكون علي الصوم من رمضان فما أستطيع أن أقضيه إلا في شعبان"

MA'ANA:

Ya kan kasance akwai ramuwar (azumin) ramadan a kaina amma ba na samun ikon rama shi har sai sha'aban ya zo.

Dan haka anan suka ce wani lokacin uzuri ya kansa A'isha ta kasa rama azumin da ke kanta har sai watan sha'aban ya zo ta ke ramawa.


 Sannan suka ce abu ne sananne ga A'isha wajen kwaɗayinta na yin nafiloli, dan haka zeyi wahala a ce wai ba tayin azumin nafila musamman kamar irin su: azumin tasu'a, azumin ashura, azumin ranar arfa, azumin sitta shawwal, da kuma azumin watan zulhijja:

2. Ƙauli na biyu shi ne, Mazhabin Malikiyyj da Shafi'iyya sun tafi a kan cewa makaruhi ne a kan wanda a ke binsa bashin azumin farilla kuma yace zeyi na nafila. Dalilinsu kuwa shi ne, suka ce mutum ya fara biyan bashin da a ke binsa na azumi shi ne yafi muhimmanci a gare shi a kan ya shagaltu da yin azumin nafila, dan haka suka ce makaruhi ne:

3. Ƙauli na uku shi ne, Mazhabin Hanabila an samu ƙauli guda biyu a wajensu, akwai ƙaulin da suka ce ya halatta sannan akwai ƙaulin da suka ce haramun ne mutum ya yi azumin nafila dole sai in ya fara rama wanda a ke binsa bashi tukuna, daga cikin dalilansu na cewa haramun ne sun kafa hujja da wannan hadisi ko da yake wasu Malamai sunce hadisin bai inganta ba:

"………ومن صام تطوعا وعليه من رمضان شيء لم يقضه لم يتقبل منه"

MA'ANA:

………Wanda ya yi azumin nafila alhali akwai wani abu na ramadan a kansa da bai rama ba to ba za a karɓa masa (azumin nafilar da ya yi ba)

To amma magana mafi inganci kamar yadda mafi yawan Malamai suka rinjayar itace, ya halatta mutum ya yi azumin nafila musamman azumin da a ka iyakanceshi da wasu raneku na musamman kamar azumin ranar arfa da sauransu, wanda idan lokacinsu ya wuce shikenan sun kuɓucewa mutum, to a nan ya halatta mutum ya yi wannan azumin ko da kuwa ana binsa bashin na farilla da bai rama ba, sai dai duk da cewa ya halatta ayi to amma abu mafi kyau shi ne an fi son mutum ya gaggauta biyan bashin da a ke binsa na farilla.

Amma idan ya kasance azumin sitta shawwal ne Malamai suka ce mutum ba zai yi ba har sai in ya fara rama wanda a ke binsa na ramadan tukuna, domin wanda ya cika azumin ramadan to shi ne idan ya yi azumin sitta shawwal za a bashi ladan kamar ya yi azumin shekara, dan haka sai Malamai suka ce wanda a ke binsa ramuwar azumi to ko da ya yi azumin sitta shawwal ba shi da lada domin shi bai kammala azumin ramadan ba.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

   Mυѕтαρнα Uѕмαи

    08032531505


Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments