HUKUNCIN YIN LAYYA DA DABBAR DA BA TA CIKIN JINSIN DABBOBIN NI'IMAH?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene hukuncin yin layya da dabbar da ba ta cikin jinsin dabbobin ni'imah?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله

    Bai Halatta yin layya da Kifi, ko Doki, ko talo-talo, ko kaza ba domin daka cikin sharadin layyah shi ne: Ta zama daka cikin dangin dabbobin Ni'ima Raƙumi saniya Tunkiya akuya

    Saboda fadin Allah maɗaukakin Sarki:

    ( Kowacce Al'umma mun sanya Musu Yanka dansu Ambaci Sunan Allah akan Abunda muka Azurtasu na dabbobin Ni'imah).

    Ba'a samo Daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ko wani daka cikin sahabbai ya yi layya da dabbar da ba ta cikin dabbobin Ni'imah.

    Duba fat-Hul ƙadeer (9/97)

    Nawawi Ya ce: Sharadin layya shi ne: Tazama daka cikin dabbobin ni'imah Raƙumi, Saniya Akuya, tunkiya

    Duba Al-Maj-Mu'u (8/364- 366)

    Kamar yanda Ibnu ƙudama ya fadi irin haka acikin Al-Mugni (368).

    Saboda Kuma layya ibadace kamar hadaya baza'ayi da wata dabba ba sai Wacce Nassi yazo daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam, Ba'a samu daka gareshi ko wani cikin Sahabbansa, da ya yi hadaya ko layya da dabbar da ba Raƙumi ko Saniya ko tunkiya ko akuya ba

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.