𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam tambayata ita ce shin matafiyi zai iya yin nafilah?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Ya kasance daga cikin shiryarwar Annabi ﷺ a lokacin da yake halin tafiyarsa, yakan taqaitu ne ga farillai, ba a kiyaye yin sallolin nafila na rawatib daga gare shi ba, wato sallolin da ake yi kafin sallar farilla ko bayan farilla, face sai kawai sallar wutiri da raka'atal fajri, ya kasance ba ya daina yin waɗannan a halin zaman gida ko a halin tafiya kamar yadda Ibnul Qayyimil Jauziyya ya faɗi.
Duba Zádul Ma'ád Fiy Hadyi Khairil Ibad, mujallad na ɗaya, shafi na 243, ɗab'in Dárul Áfáqil Árabiyya.
An tambayi Abdullahi ɗan Umar game da yin sallolin nafila a halin tafiya sai ya ce: "Na yi tafiya tare da Annabi ﷺ ban taɓa ganin sa yana yin nafila a halin tafiya ba, kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: "HAQIQA MANZON ALLAH YA ZAMANTO KYAKKYAWAN ABIN KOYI A GARE KU"" Ahzab 21.
Bukhari 1101, Muslim 689.
A taqaice dai saboda kada a tsawaita wajen kawo maganganun malamai, Annabi ﷺ yana taqaituwa ne ga sallolin farilla idan yana halin tafiya. Ta ɓangaren nafila kuwa yana yin tsayuwar dare ne da wutiri da ra'ka'atal Fajri da Sallar walha a halin tafiya. Amma sallolin nafilar da ba ya yi a halin tafiya sune na Rawátib, da suka haɗa da na kafin Azuhur da na bayan azuhur, da na kafin La'asar, da na Magriba, kamar yadda wasu malaman suka bayyana bisa dogaro a kan wasu hadisai da za mu ba da misali kamar haka:
Abuhurairata R.A ya ce: "Masoyina Manzon Allah ﷺ ya yi mini wasiyya da yin abubuwa guda uku, ba na taɓa daina su a halin tafiya ko zaman gida; raka'a biyu na walha, da yin azumi uku a wata, kuma ba zan yi barci ba sai na yi wutiri." Duba Sahihu Sunani Abiy Dawud 1269.
Wannan ya nuna halascin yin sallar Walha da Wutiri ko da a halin tafiya ne.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.