𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam Allah ya
kara basira, malam ya halatta mutum in zai yi aure a je a duba wa mutum matar
da zai aura ita ce abokiyar arzikinsa kafin ya aureta, hakan ya halatta, in
kuma bai halatta ba to malam ya hukuncin yin auren da wannan manufar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salám. Bai halasta
mutum ya je wurin kowa domin a duba masa komai na abinda ba wanda ya sani sai
Allah ba, yin hakan shirka ne da Allah, saboda ba wanda ya san cewa mata kaza
in an aure ta hakan zai zama sanadin arziki, ko ba zai zama ba sai Allah. Duk
wanda ya yi da'awar ya sani ƙarya yake yi, saboda ba wanda ya san abin da ke ɓoye
sai Allah, Allah shi ke azurta bawa, kuma shi ke jarabtarsa da akasin haka,
hikimar haka ita ce domin ya jarabci wanda aka azurta da wanda ba a azurta ɗin
ba. Don haka duk wanda zai yi aure ya dogara da Allah kawai, ya bar wa Allah zaɓinsa
in Allah ya so Allah zai zaɓa masa na gari.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Tambaya Da Amsa Abisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.