Ticker

IDAN KIRISTA YA BIYAWA MUSULMI AIKIN HAJJI, HAJJINSA INGANTACCE NE !

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum, don Allah ina da tambaya wai idan Christian ya biya ma musulmi Saudiya idan har yaje, ya ibadar sa yake?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Ya halatta arne ya biyawa Musulmi aikin Hajji, Kuma hajjinsa ingantacce ne mutukar ba da dukiyar haramun ya biya masa ba .


Annabi ﷺ ya kasance Yana karɓar kyauta daga arna, ya karɓi kyauta daga Kaisar sarkin Ruum da Mukaukis, har baiwarsa Mariya wacce ta haifa masa Ibrahim kyauta ce da ta gangaro daga kafiri.


Allah ne mafi sani.


Dr. Jamilu Yusuf Zarewa


Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments