Ticker

IDAN KWANAKIN KAFFARAR KISA SUKA RATSO A RANAR IDI, ME NE NE HUKUNCI?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum. Allah ya karama rayuwa albarka. Malam don Allah a taimakamin da amsar tambayarnan. Mutumin da yake azumin kaffarar mutuwa ya zaiyi da ranar sallah. Shin zai aje azumin na ranar ne koko zai wuce kawai da azumin shi. Allah ya bada ikon amsawa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Amin Allah ya amsa adduarka.

Malamai sun yi saɓani game da azumin kaffara idan ya ratso ranar idi zuwa maganganu guda biyu :


1. Ba za'a tsaya ba saboda ranar idi za'a cigaba da azumin saboda aya ta (92) a suratun Nisa'i ta shardanta yin azumin kaffarar Kisa a jere, dakatawa saboda idi kuma zai Kore wannan sharadin, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai. 


2. Ya wajaba ya sha azumi a ranar idi, saboda yin AZUMI haramun ne a wannan ranar kamar yadda hadisin Umar Ɗan khaddabi ya tabbatar, wannan yasa ba shi da laifi idan ya sha tun da Sharia ta yi masa izni.


Zance mafi inganci shi ne na Biyu, saboda idan hani da umarni suka ci karo da juna ana gabatar da hani, saboda haka mai kaffarar Kisa zai sha saboda Idi ko tafiya ko haila.


Don neman Karin bayani duba: Al-Muntaka min Fataawa Alfauzaan 1/152


Allah ne mafi sani. 


AMSAWA✍

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa


Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments