Ticker

6/recent/ticker-posts

INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN BUDURWATA ?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam ko ya halatta in kalli gashin macen da na ke so in aura? Ko kuma don Allah malam ka taimaka Ka min bayanin abin da ya halatta in kalla a jikin macen da zan aura kafin mu yi aure. Na gode. Allah Ya gafarta maka.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To ɗan’uwa ya halatta ka kalli macen da kake so ka aura, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa: “Idan ɗayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan” Abu dawud a hadisi mai lamba ta : 2082.

Malamai sun yi saɓani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure.

1. Akwai waɗanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai, saboda tafin hannu yana nuna ni’imar jikin mace, kamar yadda fuska take nuna kyau, don haka sai a takaita akan su, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.

2. Zai kalli duk abin yake bayyana a jikin mace, don haka bayan fuska da hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya.

3. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskance shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta. wannan ra’ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai sanin yanayin matar da zai aura, yadda ya kamata . Saidai ba’a son yawaita kallon saboda duk abin da aka halatta saboda bukata, to ya wajaba a tsaya a gwargwadonta, wannan yasa yawaita zuwa zance da yawaita yin waya, zai iya zama haramun saboda yana iya tayar da sha’awa, sha’awa tana iya kaiwa zuwa ɓarna .

Don neman karin bayani, duba : Al’insaf 8\15 da Muhallah 9\161.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments