Ticker

Ina Yawan Tunanin Lamarin Duniya Da Waswasi A Cikin Sallah!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam ina so a yi min bayani kuma a taya ni addu'a, idan ina sallah sai in shiga tunanin matsalolin rayuwa kuma abin yana damuna kuma na kiyaye da abubuwan da na ji malamai suna cewa yana kawo hakan.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, yawan yin waswasi da tunanin al'amuran duniya a cikin sallah yana rage wa sallar mutum kamala har zuwa mutum ya sallame sallarsa, amma ba ya ɓata sallar, kuma hakan na sa ba za a rubuta wa mutum komai na sallar ba face rabi ko ɗaya bisa huɗu, ko ɗaya bisa goma, kamar yadda Sheikh Ibn Uthaimeen ya bayyana.

Duba Fatáwá Nurun Alad Darb 8/2.

Hadisi ya tabbata daga Usman ɗan Abul Ási Allah ya ƙara masa yarda cewa: Shi Usman ɗin ya zo wurin Manzon Allah ﷺ sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai shaiɗan ya shiga tsakanina da sallata, yana rikita mini karatun sallata, sai Manzon Allah ﷺ ya ce: "Wannan wani shaiɗani ne da ake kiransa da Khanzab, duk lokacin da ka ji shi ka nemi tsarin Allah a kansa, ka tofa a ɓangaren hagunka sau uku", sai Usman ɗin ya ce: Sai ko na aikata hakan, sai Allah ya tafiyar da shi daga gare ni. Muslim 2203.

Wannan sai ya nuna cewa duk lokacin da mai sallah ya yawaita jin waswasi da tunanin zuci a sallarsa, to ya yi 'A'uzhu Billahi' ya tofa a ɓarin hagunsa sau uku, in Allah ya so Allah zai tafiyar masa da wannan waswasi ko yawan tunani.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments