Iyayena Sun Hana Ni Aure Wai Sai Nayi Karatu Mai Zurfi Kuma Ina Da Tsakanin Sha'awa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum inama malan fatan alkhairi dan Allah shawara nake nema na kasance mace mai karfin sha'awa tun tasowata gashi iyayena wai sai mun yi karatu me zurfi hartakaiga inasa hannu a farjina idan nasa nakanji kwanciyar hankali kuma idan nayi istigfari akan natuba sai nakoma saboda wahalar ciwon da nakeji natuba yafi sau nawa dan Allah aban shawara nagode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalam warahatullah.

    To 'Yar uwa wannan matsalar tana damun matasa maza da mata wato matsalar rashin Aure, kuma wannan sa hannu a farji, saɓawa ALLAH ta'ala ne, gaskiya kuma shawaran da nake baki anan ita ce.

    Na farko kidena zama a Ɗaki ke kaɗai Sannan ki yawaita Azumin nafila domin Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) yace yana rage ƙarfin sha'awa.

    Sannan ki yawaita karatun Alƙur'ani shima wannan babban magani ne. Ki yawaita Istigfári, kuma shi ƙofar tubanki tana nan a buɗe kamar yadda wannan hadisin ya nuna

     كل بني ادم خطاء وخير الخطاءين التوابون

    "Dukkan 'yan adam masu saɓone, mafi alherin masu saɓo, sune masu tuba"

    Dan haka ki tuba kiyi nadama akan cewa ba za ki ƙara komawa zuwa ga wannan saɓon ba In shã Allahu, Allah ze yafe miki.

    Anan muke kira ga iyaye wallahil azeem kuji tsoran ALLAH idan anzo neman Auren 'yayan ku, Ku bayar idan ba haka ba wallahi zaku haifar da fitina a bayan ƙasa domin a sanadin kaƙi yiwa 'yarka Aure taje ta fada ZINA !! to lallai kai ne sanadi kuma kanada naka kason Na zunibi.

    Duk Wanda akazo Neman Aure Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce: Ku kalli addinin sa kawai Ku bashi idan kunƙi fitina zata haifu a ban ƙasa.

    Wallahi saɓawa maganar Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) dedai yake da Saɓawa ALLAH.

    ALLAH ta'ala ya tsaremu

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.