Ticker

Karanta Alƙur'ani Da Nufin Allah Ya Kai Wa Mamaci Ladar!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah... Dan Allah zan yi iya karanta wata surah a Kur'ani... Misali suratul Mulk da niyyar Allah ya kai ladar ma mahaifina?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám, Malaman Musulunci sun tafka saɓanin fahimta zuwa gida biyu game da hukuncin karanta Alƙur'ani da nufin Allah ya kai wa mamaci ladar. An yi wa Shaikh Abdul'aziz bin Baaz makamanciyar wannan tambayar sai ya ba da amsa da cewa: "Karanta Alƙur'ani da nufin ladar ya kai zuwa ga mamaci, malamai sun yi saɓani game da hakan; daga cikin malamai akwai wanda yake fahimtar halascin hakan, kuma yake ganin mustahabbi ne, har ma ya ce: tabbas ladar tana iske mamata, kuma tana amfanar su, wannan fahimtar sananniya ce a mazhabar Ahmad da jama'ansa, wasu malaman sun hakaito hakan, kuma shi ne maganar jumhurun malamai, Ibnul Ƙayyim ma ya tabbatar da hakan a cikin littafin ARRUHU, kuma ya tsawaita bayani a kan hakan".

Sai Shaikh ya ci gaba da cewa:

"Wasu malaman kuma suka ce: Lallai nema wa mamaci lada da karatun Alƙur'ani ba a shar'anta hakan ba, kuma ladar ba ta iske shi, an ruwaito hakan daga Ashafi'iy Allah ya yi masa rahama, da wasu jama'an daga cikin magabata, kuma wannan fahimtar ita ce ta fi inganci, saboda rashin dalilin yin hakan, domin ibadoji tauƙeefiyya ce (ba a yi sai Shari'a ta tabbatar), ba da lada ga mamaci nau'i ne na ibada, bai kamata a yi ba sai da dalili, ba mu san wani dalili bayyananne a Shari'a da ya nuna mutum zai yi ma waninsa sallah, ko zai yi ma waninsa karatun Alƙur'ani ba...".

Ya ci gaba da cewa:

"Sai dai ya yi masu addu'a, ya nema masu gafara, ya nema masu rahama, kuma ya yi masu sadaƙa, babu laifi ga hakan, kuma ba muna cewa: yin hakan bid'a ba ne, ba muna cewa: haramun ba ne, muna cewa ne: wannan fahimtar ita ta fi, kuma tafi dacewa..."

Duba Fataawá Nurun Aladdarb (14/196, 197), na Ibn Baaz.

Ko a duba Fataawal Lajnatid Dá'ima (2/204, 205). Almajmu'a ta biyu. Don neman ƙarin bayani.

Saboda haka, ‘yar uwa lamarin karanta Alƙur'ani da nufin Allah ya kai wa mamaci ladar, lamari ne da malamai suka sami saɓanin fahimta a kai, kuma ficewa daga cikin saɓanin malamai, da komawa kan abin da malaman suka haɗu a kai ya fi samar da natsuwa da inganci.

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments