Ticker

Kishi Rahama Ne Ko Azaba //05

v) Kafofin sadarwa: Kafofin sadarwa da rubuce-rubuce a shafukansu ko a littafai na da gudummuwoyin da suke badawa wajen daga kishin mace a kan namiji, shin a manyan kafofin sadarwa ne ko kuma a na zamani? Akwai shirye-shirye na masamman da ake gabatarwa a kan zamantakewar miji da mata, da wasu da suka shafi matan zalla, da kuma irin rashin gaskiya da barnar da mazaje ke yi a gari, sukan saka shakku a zuciyar uwargida idan ta gani.

Haka su ma mazan idan suka ga abubuwan da matan ke yi a wuraren aiki da maganganun da ake yi kansu a kafafen sadarwa dole shakku su shiga ƙirazan mazan nan take kishi zai sami wurin tsuguno. A 'yan shekarun baya an yi ta gutsiri tsoma kan ma'amalar dake tsakanin ma'aikatan asibiti mazansu da matansu, bisa wannan dalilin ya sa wasu aurarrakin suka sami tangarda don mazan sun fara shakku na ganin alƙaluman da aka fada na alaƙar mazan da matan, ga su kuma matansu na aikin.

Sannan ga kafafen sada-zumunta irin su WhatsApp da Instagram da Tiktok da sauransu inda matan aure ke caba ado na kalli-ka-ƙara su yi hoto, kuma su dora kowa ya gani, wannan na dada sa wa wasu mazan su fara tunanin kar dai a ce matansu ma na yin haka! Sai su fara bincika wayoyin matan, domin akwai nau'i na rashin kishi in aka ce namiji ya ba da dama irin wannan ya faru a cikin iyalinsa bai dauki mataki ba, kishi ya taso kenan. Tabbas akwai mazan da ba su da kishi, tare suke yin hotunan da matan kuma sun san cewa za su dora a kafar sada zumunta amma ba za su damu ba.

Akwai kuma wasu wasannin kwaikwayo masu dogon zango da a cikinsu ake nuna irin dabi'un maza na ha'inci, wani yana tare da iyalinsa cikin rashi da wadata tana haƙuri da shi, yau a ci gobe a rasa, ta sa kudinta ta sayo, ashe dan matalikin kudi yake kashe wa wata a waje ba kadan ba, in mata na ganin wannan dole su fara bincikar maigidansu shin shi ma yana samu ne ya kai wa ballagaza bayan ga su a cikin gida da yara cikin yunwa? Da zarar ya bayyana cewa yana neman wata ko yana da alaƙa da ita to nan take kishin zai bayyana.

Akwai kuma shirye-shirye na wayar da kan matan da ake gudanarwa a rubuce ko a kan akwatin talabijin, a ciki akan gayyato ƙwararru da masana kan al'amuran zamantakewa. Suma sukan fadi irin wahalhalun da mata kan sha da namiji, amma da zarar wadata ko wata faraga ta samu a maimakon ya yalwata iyalin sai ya fara neman aure. Su ma wadannan shirye-shirye kan yi matuƙar tasiri a zukatan matan kuma sukan motsa kishinsu sosai domin masana ne ke yin bayani, kuma galibin abubuwan da suke fadi kan bayyana musu, dole su gasgata duk abubuwan da suke ji.

Ba wannan kadai ba, akwai wasu zauruka na mata, inda za ka taras suna sakin baki abinsu da tunanin cewa su kadai ne a ciki, sukan yi duk maganganun da suka ga dama, anan ne wata kan dauki wasiyoyin shedan ta sami damar yin rigima da maigidanta, a ƙarshe a ce kishi ne. ko da yake wasu mazan in suka sami matan da laushi ba sa kyautatawa. Na ga namijin da ya kawo wace zai aura gidan matarsa, kuma ya ce ta yi musu abinci, wata za ta yi ba za ta damu ba, wata kuwa ƙaramin yaƙi za a yi a cikin gidan.

A wannan karon dai uwargidan ba ta dafa abincin ba, maigidan ya tashi da kansa ya dafa, uwargidan ta kwashe kaf ta raba wa maƙwabta bai sani ba, ya shigo ya taras da kwano, tana cikin gidan ta ce ba ta san  abin da ya faru ba. Dariya ya yi kawai ya bar mata gidan, amma an ce ya kashe kudi da yawa a girkin. Wata da ta ji maganar cewa ta yi da kayan wa aka dafa abincin? Aka ce da na uwargidan sai ta girgiza kai kawai ba ta yi magana ba, ke nan da ita ce za a sha kallo. Duk wannan fa amaryar da za a kawo din cewa ta yi ba ma za ta ci ba.

Ba na tantamar cewa kafofin sadarwa na koya wa mata yadda za su gyara kansu da gidajensu, da yadda za su riƙa shiga don maigida da ma yadda za su yanayin maganarsu da shi a matsayin mata da miji, wannan zai amfani mai yin kyakkyawan kishi, don duk  abin da maigida yake so wanda zai iya hangowa a waje matar dake cikin gida za ta iya kallo kuma za ta gyara in tana da buƙatar hakan, amma ta ce za ta yi fito na fito da yaran yanzu ba tare da ta gyara matsalolinta ba ba na jin hakan zai haifar mata da da mai ido.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments