2) Hassada da Wahalar da kai: Kafin mu shiga wannan yana da kyau mu yi ƙoƙarin rarrabe wasu kalmomi:-
a) Hassada:
Ita hassada takan sa mutum ne ya yi ta fatar kar dan uwansa ya sami alkhairi,
ko kuma in ma ya samu din ta yi sanadin da zai rasa.
b) Fata: Ita fata
a wannan babin tana nuna yadda mutum yake kwadayin shi ma ya sami kwatankwacin abin da dan uwansa ya samu ne, ba tare da
burin dan uwan ya rasa ko kar ya samu ba.
c) Kishi:
Wannan in ya zama mummuna ba komai a cikinsa sai son kai, wato "Kowa ya
rasa in ba ni ba".
To mace mai
mummunan kishi za ka iske ta cikin damuwa, ta rasa kudinta, kyawunta, ƙaunar
jama'a, zaton alkhairi duk a banza. Zatonta kullum ana yi mata kaza da kaza, ko
kuma don me za a yi wa wance kaza? Inda hassada ke shiga shi ne lokacin da take
ƙoƙarin kishiyarya ta rasa abin da ta
samu, ko da kuwa haihuwa ce ko wani farin ciki. Hassada kan garwayu da kishi
kamar yadda kowanne kan kama hanyarsa; idan mace ta je maƙe tana son ta ji
motsin kishiyarta da maigidanta a shimfida, ko tana son ta ji me suke cewa, tambayar
anan: Me zai amfane ta?
In dai tana yi
ne don zafin da take ji, me ya sa zai je wajen wata bayan ga ta? Wannan dora wa
kai ne matsala don za ta ji abin da ba
zai yi mata dadi ba, kuma zai ci gaba da damunta a zuciya, amma idan ya kasance
tana baƙin cikin yadda za a je wajen wata ne bayan ga ta, hakan ya kai ta ga
shiga malamai don yadda mijin zai ƙyamaci wancan ai kun ga an yi asara, a ƙarshe
ta dena yi wa abokiyar zaman fatar alkhairi to wannan hassada ce zalla.
A kowani
lokaci in kishi ya yi wa mace yawa yakan dora mata matsalolin rayuwa da dama,
ita ce lura da kai-komon mijinta, 'yan uwanta hatta oganta a wurin aiki. Da
yawa za ka ji ma'aikaciya na rigima da wasu a kan oganta kuma ba mijinta ba fa,
abin haushi kowanne cikinsu na da abokan zama, ita tana da miji shi ma yana da
iyalinsa kuma ba ma ita ce a gabansa ba. Duk wanda ya zo wurinsa sai ta yi ƙoƙarin
sanin me ya kawo shi? To bare ta ga wata mace na yawan shiga wurinsa, ba fa son
sa take na mace da namiji ba tsabar kishin ne kawai.
Galibin waɗanda
take kishin da su kan hada har da 'yan uwanta mata, masamman ƙanwarta idan taga
tana kusantar saurayinta, na dai san an taba yin wace ta haƙura ƙanwarta ta ƙwace
saurayinta. Uwayen sun yi ƙoƙarin hanawa ko kuma kowa ya rasa tunda sun san
yadda abin ya faru, amma da yake kishin yayar da sauƙi ta yi aiki da hankali ta
yi magana masu dadi waɗanda da su ta iya gamsar da uwayen suka haƙura.
Ta ce "Ni
fa ina neman miji ne ba namiji ba, wanda zai zo wurina ya ƙare wa ƙanwata bai
dace da ni ba, ko na aure shi hankalinsa ba shi a kaina tunda ya nuna wace yake
so, a ƙarshe zan auro mana shi ne ni da ita, sun riga sun shaƙu ni ina gida su
suna waje, da a ce zuciyarsa na kaina ne shi ya kamata ya yi maganinta kafin
kowa ma ya sani" haka ta bar wa ƙanwar shi, kamar ba a taba yin kamarsa
ba, kishinta da sauƙi kuma ta sami zaman lafiya.
Mace mai mugun
kishi kan wahalar da ƙwaƙwalwarta wurin tunani, ta wahalar da jikinta gaba
daya, ita ke nan maƙe don da ji me ake cewa, takan yi wasu ayyukan ba don tana
so ba, kawai don ta wahalar da kishiya ko don kar mijinta ya yi wata matar. Bar
batun bin bokaye, akwai wace kan tashi ta wanke wa mijin mota ta yi kaza da
kaza duk akwai masu yi, don dai kawai wata ta shiga matsala ko don kar wata ta
shigo mata. Akwai wace za ta cika kudin cefane daga aljuhunta, ta rantse wa
mijin dan kudin da ya bayar ne ya yi haka tunda ta san kishiyar ba za ta iya
haka ba.
Ƙwaƙwalwarta
ba ta hutu "Yanzu haka ya tafi wurin wata ne, me yake yi a waje?" In
waya ya bari ta dauka ta yi ta leƙe-leƙe ko yana magana da wata. Ko waya ya
daga sai ta zo wurin ta ji da wa zai yi magana, kuma me zai ce? Ko abokansa
yake hira da su sai ta tabbatar ba ba shi shawara suke yi ya ƙara aure ba. A kullum
cikin damuwar ƙila za a yi mata kishiya, in ta san yana wasa da wata to
matsalolinta sun ƙaru.
(Kar ku yi min
dariya) ina matashi na taba son wata abokiyar karatuna, ta fi ƙarfina a komai
tabbas. Sunan wanda ya aure ta yananan a ƙwaƙwalwata har yanzu, mun gama karatu
na dawo gida wani yaro ƙanin abokina ya zo ina wasa da shi, na tambayi sunansa
aka ce "Wane" sunan abokin hamayyana, take na kori yaron, abokaina
suka yi ta yi min dariya har yanzu ban manta ba. Mace mai uban kishi ta
wucenan, don lokacin da za ta yi addini da hankali ba aunin gwada kalmominta ba
ne. Duk abin da ya fito bakinta fadinsa
za ta yi.
Anan Zan
Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.