Kishi Rahama Ne Ko Azaba //09

    4) RUSA GIDA: In kana neman  abin da ke wargaza gida daga sama har Æ™asa da ka sami kishi daya kenan, Æ™ila ma ba ka da buÆ™atar neman wani. A duk lokacin da muka kira wani mummunan abu muka hada shi da kishi to mummunan kishi muke nufi, shi ne wani lokaci maza ba sa gane shi, har sai ya yi lahanin da ba zai taba gyaruwa ba. Wata macen kan sa namiji ya kori uwar 'ya'yansa kuma ba za ta iya riÆ™e su ba, kwanannan ba a yi shekara ba wata ta bar gidanta ta auri wani amma ta kasa riÆ™e masa 'ya'yansa, ita ma inda ta bari din wata ta kasa riÆ™e mata nata, dukansu ba wace ba a sake ta ba. Wannan ba wani abu ne ba banda son kai wanda shi ake kira kishi.

    Da mace na da wayau ai an bar mata 'ya'ya kyauta yadda za ta tarbiyantar da su ta fuskar da take so, ta kuma ci gajiyarsu, amma baÆ™in kishi ya hana. Irin wannan kishin kan sa namiji ya rabu da 'yan uwansa, yadda mace za ta shiga tsakiya daga ita sai maigidanta, ba ruwanta da 'ya'yan kishiya ma bare 'yan uwansa. Na taba jin wata na sumbatu wai duk  abin da take wa 'yan uwan mijin ba sa gani, ba ta san me ya sa suke son shiga mata sha'anin gidanta ba. Ta manta cewa ita ce aka auro, waÉ—anda take ganin bare su ne masu gidan, mutuwa ko saki daya zai sa ta kama gabanta ta bar musu gidan.

    Shekarun baya wasu yara suka kawo min kukan babansu, ya yi ritaya ya karbi kudinsa ya bude shago yana zama a ciki, amma ba su isa ko biskit su samu a shagon ba, sai dai 'ya'yan kishiyar mamansu, a Æ™arshe ma ta hana su zuwa gidan gaba daya da yake duk sun yi aure. In suna son ganinsa sai dai su same shi a shago, in wani abu zai ba su dole sai a gabanta, kuma sai  abin da ta ce a bayar, duk  abin da ya ba su sai ta sa an rage wai yaranta fa? Ta kakkame komai, wani sa'in sai dai baban nasu ya saci ciki ya fita in zai ba su wani abu ya ba su a waje in ba haka ba matar ta hana.

    Yarinyar ta ce "Babban  abin da ya saka ni kuka shi ne yadda na sami babana a shago na zauna cikin farin ciki muna ta hira da zan tashi ya dauko (abu) ya ba ni, ashe a kan idonta ne ta hango, kamo hanya da ta yi ya ganta, ai kuwa ya Æ™wace ya fara ce min: Fita-fita, maza ki je gida na gaji haka. Haka dole na fita ina kuka" daganan ta ce gidan ya ishe su gaba daya ba sa ma sha'awar zuwa, tunda uwarsu ma ta dade da rasuwa uban kuma ba ya buÆ™atarsu.

    Duk tambayoyin da na yi mata ta ba da amsa da kanta cewa babansu na son su, amma kishiyar mamansu ce ba ta buÆ™atar ganinsu a gidan gaba daya, kuma ta yi duk  abin da za ta yi ta raba su da gidan, ta tabbatar wa uban da cewa to fa 'ya'yansa ke nan wadannan dake gabansa, sauran kuma oho. Na ce mata "A gidanku duk kuka girma?" Ta ce "I" "Kuna zaman lafiya da mazajenku?" Ta ce "Alhamdu lillah duk mazajensu sun san matsalolinsu kuma suna iya bakin Æ™oÆ™arinsu"

    Daganan na ce "To ku gode wa Allah ku miÆ™a masa lamarin, babu  abin da bai da iyaka ba zai bari ya wuce haka kawai ba" wannan fa ya fi sauÆ™i sama da wace ta ga ba ta da yara ta sa mijin ya sayar da gidan ya kama musu haya, ta karbe kudin ta Æ™ara gaba ta bar shi da uwargida da dumbin yara, a ganinta ta cutar da kishiyar. Wata kuwa ta kai yadda maigidan ya ja wa 'yan uwansa layi da cewa kar wata ko wani daga cikinsu ya Æ™ara taka masa gida ko ya tambaye shi wani abu, Æ™ila anan a ce sun ci riba amma gaba fa?

    Wanda ya fi muni a duk wadannan shi ne wanda matan za su hana 'ya'yansu su yi zumunci, ƙila wanda ake kishin dominsa ya mutu, yaran kuma su taso kansu a rabe, mutum da dan uwansa amma ya fi son ya kyautata wa bare, in da dan uwan zai sami wani budi daga Allah sai ka ga ransa ya baci sam bai yi masa fatar alkhairi, ya gaji mummunan kishi daga mahaifiyarsa. Da za ka tsare shi ka tambaye shi me ya yi masa bai da kalmar da zai iya gaya maka, sai dai ya yi ta kame-kame, mummunan kishi ne kawai da aka gada daga mahaifa.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.