Kishi Rahama Ne Ko Azaba //12

    ALAƘAR SHEDAN DA KISHI

    Gaskiya in za a tabi wannan batun sai an raba shi zuwa gida biyu, wato shedanin aljani da na mutum.

    1) Wasu lokutan in mace na da iska sukan ce za su taimaka mata, dan  abin da bai taka kara ya karya ba za ka ga mai aljanu tana rigima da mutane, wannan cuta ce kuma akan yi magani a sami lafiya, akwai shedanun aljannu dake sanya mace ta riÆ™a wasu ayayyakai na mummunan kishi har ya kai inda maigidan zai gaji da ita ya sake ta, yadda a Æ™arshe za ta ci gaba da zama ita kadai ba tare da namiji ba.  abin da suke so ke nan kuma samu.

    2) Wasu lokutan ba iskar ce da kanta ta kama mace ba, bokaye ne suka tura mata kamar yadda wata ko wani suka nema, in daga mace ne to mummunan kishi ne kan sa ta nemi a tura mata, in kuwa namiji ne ya kasu kashi biyu; kodai ya sa a tura mata don ta rabu da wancan ta dawo masa, ko kuma ya dauki matakin ranuko da tunanin ta yaudare shi, yadda ya rasa ta ita ma ta rasa wancan. In har za a je gaban boka dama ba maganar imani ake yi ba bare a ce za a yi maganar  abin da ya dace a shari'a. Sai dai a ga mace na yin  abin da bai kamata ba a ce ta cika zazzafan kishi.

    To da yake kowa ya san hakan na faruwa mata kan yi amfani shi wurin aikata barnar da suke so, a ƙarshe su ce magani aka yi musu ba da son ransu ba ne, a gaskiya ba wani magani son kai ne kawai da aka fassara shi da kishi. Wata kan fara dauke-dauke, tabbas akan yi wa mace sihiri ta yi hakan don a raba ta da maigidanta, sai dai wata halinta ne, yadda ake ganewa kuwa sanin mutum da dabi'arsa kafin aure, ko kafin zama da kishiya. Mai halin dan bera bai iya rabuwa da halinsa.

    Wata akan saka ta ƙazanta ne, a duk sha'aninta babu tsabta, duka dai ana iya ganewa ta yadda aka san mace a dabi'arta tun tale-tale. Haka saurin fushi da gaba da mijin ba gaira ba dalili. Ni dai a tawa masaniyar an yi wasu masoya da kowa ya tabbatar da yadda suke ƙaunar junansu amma dab da auren sai komai ya lalace, uwayen suka ce ba gudu ba ja da baya, me ya sa ta bari tuntuni ba ta yi wani abu ba sai yanzu da ta ga an zo aure? Suka ce ba za ta raina musu hankali ba.

    To an daura auren amma da zarar ya kusa da inda take sai komai zai canza, sai ta daure masa. Mutane na ganin kamar shegantaka ce kawai tunda ta fara nuna ba ta son auren dab da lokacin. Ina ganinta na fahimci akwai matsala, na kuma ba su shawarar neman magani, cikin ikon Allah an sami karbuwa da ga Allah ta warke sarai. ke nan wasu ayiyyukan ba fada ko wa'azi ke maganinsu ba, a Islamic kemis za a samu.

    Bari ki ga inda shedanun mutane ke taka rawa wurin fitar da mace daga gidanta, wata ce Æ™awayenta suka yi ta zuga ta cewa maigidanta na yin kaza da kaza, ita ce fa tare da shi, amma tana jira waÉ—anda ke nesa su ne za su gaya mata ga yadda yake ga  abin da yake yi. Haka suka yi ta ingiza ta tana tara masa baÆ™in ciki har ya gaji ya sake ta ta dawo gida, a Æ™arshe ya auri daya daga cikinsu. Tambayar anan da ma suna son su fitar da ita ne ko kuwa daga baya sun fahimci duk  abin da yake yi bai kai a yi kishin da mace za ta Æ™i zama da namiji ba ne?

    Ba a cewa akwai shedanun uwaye, amma tabbas akwai uwayen dake korar 'ya'yansu daga gidajensu. Babban  abin da zai ba ka mamaki ta ina mace za ta saka wa mijin 'yarta ido har wani lokaci ta shiga tsakiya tana hukunci wai yana neman mata? Kuma a daidai wannan lokacin tana tare da fahimtar diyarta wace ta gaya mata komai na abubuwan da mijin yake yi mata kuma suka zage shi gaba daya wai kuma bayan ya zo ne za ta yi hukunci! Daya daga cikin dalilan da suka sa ba a son mace ta riÆ™e gida kenan, domin wannan in ba a yi sa'a ba ita za ta ba ta auren.

    Maƙwabta ma kan zuga mace ta yi ta yi wa maigidanta dibar albarka da sunan kishi. Wanda ya fi ba da haushi shi ne yadda wata nurse da maƙwabciyarta da suka zauna a gidan haya tare, ta riƙa ganin yadda nurse din take sakaci da mijin, haka ta shige masa a hankali har ta samo shi, kishin wancan ya raba ta da gidanta, ita kuma ta kashe aurenta ta aure shi. Meye wannan in ba shedanci ba?

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.