Kishi Rahama Ne Ko Azaba //13

    ME BAƘIN KISHI KE KAWOWA

    1) MUMMUNAR SHAƘUWA:  abin da ya sa aka kira ta da mummuna kuwa domin duk  abin da ya wuce iyakar da ake buÆ™atarsa bai da amfani, kamar gishiri a miya, ko sukari a zobo, ko sanyi a ruwa, ko yaji a abinci, na yi zamani da macen da ba ta iya barin mijinta ya tafi wurin aiki sai dai ta dauki yarinyarsu su tafi tare, ba za ta iya zama a gida ba, malami ne mai koyarwa, duk ajin da zai koyar tana ciki, ga shi ba shi da dama ya yi magana da dalibansa mata, masamman waÉ—anda suka saba kafin ma ya san ta. Su kuma da suka gano dabi'arta sai suka fara yin wasu abubuwa don tura mata haushi, kan ka ce wani abu alaÆ™ar ma'auratan ta fara neman tabarbarewa. Kishi na neman ba ta gida.

    2) SAURIN HASALA KAN  abin da BABU TABBAS: Da zarar dayan masoya ya ga  abin da bai da tabbas a kai nan da nan zai dauki zafi, wata Æ™ila ma ya dauki hukuncin da zai dawo yana nadama daga baya: Kamar matar da ta soka wa mijinta wuÆ™a saboda ta kama shi da wata, wai ya ci amanarta! Ga shi ya mutu ya bar ta da yara, in suka girma me za ta ce musu? "Ubanku manemin mata ne shi ya sa na kashe shi!" Ko wannan ya isa, to bare kuma ita ma za a kashe ta su bar yaran marayu, kuma za a gaya musu cewa ta keshe ubansu. Kishi bai amfani ba.

    3) KIBIYA MAI LAHANI: Irin wannan kishin kan sa masoyi ya ba ta masoyinsa, domin a Æ™arshe matar za ta kira mijinta da manemin mata ne, amma duk da haka ba za ta fita ba, kuma ba za ta bari wata ta shigo su rayu tare ba. Haka shi ma zai fara bibiyarta duk inda za ta, ko ya fara saka wa a yi masa bincike, anan me zai fara zuwa Æ™waÆ™walwar waÉ—anda aka saka su sanya mata ido? In dai akwai gasgata juna me zai kawo bincike? Matsalar irin wannan da wahala ka ga mutum na abu bai yi fatar ya ga ya cimma  abin da yake son gani ba.

    4) MANTAWA DA ALKHAIRI: A duk lokacin da mai kishi ta fara fitar da  abin da ke cikinta da wahala ta fadi alkhairin wanda take suka. An yi wata da ta kawo Æ™arar mijinta, sai mahaifinta ya ce gaskiya bai ji dadin  abin da maigidanta yake yi ba, kuma ba zai bari a jajubo masa  abin da zai ba ta masa zuriya ba, don haka ta yi zamanta zai sa a kirawo shi in gari ya waye a raba auren. ko da gari ya waye sai mahaifiyarta ce ke gaya masa cewa "Ta koma dakinta tun daren jiya" kai da ji ka san da ma uban ba da gaske yake yi ba kuma ya san  abin da zai faru kenan.

    5) WUCE GONA DA IRI: Shi ne mace ta fara addu'ar kar Allah ya yi wa maigidanta wadata ko kar ya ba shi wani aiki don kar ya sami  abin da zai yi mata kishiya. Ko ta ce ba zai fita ba sai ta san inda zai je da  abin da zai kai shi. Daga cikin irin wadannan matan akwai wace ba ta Æ™aunar ta ga maigidanta ya saka kaya mai kyau saboda kar wata ta gan sa ta yi sha'awa. Dan jinkirin dawowa in ya yi sai ta ji inda ya tsaya da dalilin hakan, ko Æ™anwarsa da suke uwa daya da shi ba ta so ta ga sun zauna suna hira suna dariya bare sauran dangi.

    A irin wannan wasu mazan ka yi na su, ko da yake kishin namiji addini ma ya kwadaitar da shi, amma za ka ga wasu abubuwan ko malaman addinin ma ba sa hakan. Na ga wanda matarsa ta zo yin hoto a wurin ƙidaya, amma fa bai yarda jami'in ya kalle ta lokacin da zai dauki hotonta ba. Ya ce a dauke ta da niƙabin, malamin ya ce "Kodai ta daga ko a fasa" haka ya yi ta nuƙu-nuƙu yana kakkare ta kar a ganta, ga shi a cikin layin mata yana kallon matan wasu lokacin da yake ƙoƙarin kare ta shi. A ƙarshe dai ta daga niƙabin yana ta tafarfasa.

    6) KISHI DA MAKUSANTAN MIJI: Lokacin da mace ta fara kishi da uwar-miji, ko mahaifinsa da wahala ta fada wa mijin alkhairinsa. In kuma mai shige-shige ce ta tura masa aljani da zai riÆ™a juya shi a duk  abin da take so. In ya yi niyyar kyautata wa mahaifinsa ta ce kar a yi an gama kenan. Bisa wadannan dalilan ya sa wata uwar-mijin kan dafa abincinta alhali ga matar danta na zaune, komai nata ita ke yi ga masifar uwargidar. Wata kan hana maigidan ya kyautata wa mahaifinsa ma, amma in ya yi wa nata ta yi godiya.

    Mun sami wace ba ta Æ™aunar maigidanta ya shiga wurin mahaifiyarsa bare ya ba ta wani abu. Da zai ce ya ci wani abu a wurinta ranar matar tasa ba za ta yi magana da shi ba. In wani abu ya yi mata ta nuna godiyarta ya kuskura ya ce mahaifiyarsa ta ba da shawarar a yi to in ba sa'a aka ci ba sai dai ya sa hannunsa ya dauki  abin da ya kawo da kansa. Wannan kam mummunan kishi ne ba ko shakka. Ko za ta yi da Æ™anninsa mata ko wasu makusanta wannan kam daban, amma da uwayensa abin ya baci.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.