Ticker

Kishi Rahama Ne Ko Azaba //15

9) ƘONA KAI: Wani kishin jefa kai ne a halin ƙaƙa-ni-kayi, da mace za ta tsaya ta karanci lamarin sosai ko ta dube shi da idon basira za ta gano cewa haƙuri da kishin shi ya fi. Misali: Na san namijin da mace daya ko biyu ba su isansa a shimfida sai ya faro daga dakin ta farko zuwa ta biyu ya ƙare a dakin mai girki duk dare. A ƙarshe dayansu ta ga ba za ta iya rayuwa da shi ba ta cika rigarta da iska, ganin haka ya nemo wata yarinya ƙarama wace take iya daidai da shi, tun daganan ya huda da biye-biye, a irin wannan me zai sa mace ta ce sam ba za a yi mata kishiya ba za ta jure duk wahala?

Akwai wata da ke wa mijin wanki da guga ta wanke masa mota, ga hidundumun gida ga na yara, me zai sa ta ce ta ji ta gani za ta iya komai? Da fa zai auro wata za ta huta sai kuma ranarta ta sake juyowa, nau'i ne na ƙona kai ta ce ita fa lallai komai za ta iya ba ta da matsala. Wata ma bayan duk wadannan hidundumun hatta fita kasuwannan da kanta za ta yi. Wata takan ce gwara a dauko mata 'yar aiki ta rage mata amma ba ta yarda da kishiya ba, ko da ta san mijin na dan leƙe-leƙe.

Wannan maganar ba kowa ce mace za ta iya ganewa ba, bari na yi miki dalla-dalla: Lokacin da nake makaranta wani ya kawo mana kukan wata mata mai bala'in kishi wace ba ta yarda a ƙaro mata kishiya ba, kuma ba ta iya ririta mijin kamar yadda ya kamata. Ranar da ya gaya mata gazawarta da dalilin da ya sa dole sai ya yi mata kishiya ranar ta tayar da ƙayar baya, har ta ce ga shinan da yara in ita ba ta ishe shi ba, amma ba zai kawo mata wata cikin gida ba. ko da yake ba Bahaushiya ba ce amma musulma ce. Wannan wani irin kishi ne? A ganinki ba za ta iya kisar kai a dalilinsa ba?

Wata tunda ta ga maigidan zai ƙara aure ta tayar da hankalinta, rigimar yau daban ta gobe daban, ta ba ta da duk waɗanda bai dace ta sami matsala da su ba, kuma ta nuna cewa za ta iya ƙasƙantar da kanta a komai amma kar mijin ya ƙaro mata wata matar. Shi kuma ya ce haƙurin da ya yi a baya ya ishe shi zai yi aurensa komai ta fanjama-fanjam. Ta ja kunnensa da cewa za ta kashe kanta, gwara ta mutu da ta ga wannan mummunar ranar. Magana ta kai har zuwa ga mahaifanta kuma sun shiga tsakiya suka nuna mata ba ta da hurumin da za ta hana mijinta aure matuƙar yana da niyyar hakan. Wannan ya sa ta kashe kanta saboda gudun bacin rai.

Ni nakan fahimci wannan wautar cikin sauƙi, wace samsam ba na fahimtarta ita ce macen da za ta kashe wani saboda kishi. Misali in aka ce za a yi mata kishiya sai ta kashe kishiyar, a ƙarshe kuma sakamakon kisar ko ba a kashe ta ba za ta ƙare a gidan yari, wato ita ma ta bar gidan mijin. To meye amfanin wannan kishin? In ta yi ne don ta rayu da maigidan ko bai sake ta ba hukuma ba za ta bar ta a gidansa ba, tanacan tana shan azaba a kurkuku ga wulaƙanci da bacin suna ga damuwa sakamakon kisar rai. Bare kuma daga ranar ko za ta fito maigidan ba zai zauna da ita ba.

A daidai wannan gabar yana da kyau a rabe tsakanin masifaffiyar ƙauna da kuma son kai, macen dake masifar son mijinta shi din kawai take kallo, duk  abin da zai amfane shi tana wurin, ko da kuwa auren zai ƙara, za ta iya batawa da kowa don ganin farin cikin maigidanta, mun ga waɗanda ko uwayenta ba sa iya yi da shi a gabanta, sai in ta bar wurin, abin mamaki ba  abin da yake ba ta tsabar ƙaunarsa ce kawai.

Irin wadannan matan duk da wannan ƙaunar ƙwaƙwalwarsu kan nuna musu mahimmancin uwayen miji, da 'yan uwansa, duk sukan riƙe su don kar su saba da mijin, idan suka ga hankalinsa ya karkata ga sai ya ƙaro aure, sukan yi ƙoƙarin riƙe shi ta bangaren da suka san yana da rauni don ci gaba da rayuwa da shi. Na taba ganin wace aka tambaya "Wa kika fi so da ƙauna wanda ba ki son rabuwa da shi ko da da ƙiftawar ido ne?"

.

Na zaci zan ji ta ce "Uwata" galibin amsar mata kenan, ko su ce "Uba" maza ne ake samun kaso mai girma da suke iya cewa "Iyalina" kai tsaye. Amma matannan ta ce "Maigidana, uban 'ya'yana" na so dan jaridan ya tambaye ta dalili, sai ya yi mata wata tambayar. Ita ina ta bar kishin? Ba ita ce ta biyu ba, ita ce ta farko? Duk dadewar da mace za ta yi a gidanka in ka ji ta ce "Gidammu" gidan mahaifanta take nufi. To wanda za a yi mummunan kishi a kansa ya cancanci ya zama maigida ko da yaushe. Son kai kuwa mace ta ce: Ba za a ƙaro mata kishiya ba. Ita kadai za ta rayu in ba haka ba ta janye duk  abin da take masa.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments