Ticker

Kishi Rahama Ne Ko Azaba //16

Ƙofofin Kishi Da Makullansu.

Kishi na da wasu ƙofofi da suke bude amma ana iya kulke su, in aka ci nasarar kulle su ko da za a yi kishin zai zo da sauƙi, domin dama hanya yake buƙata da zai isa zuwa ga ma'aurata to an toshe su shi kenan.


1) ZATO: Ko shedanun mutane da suke cin nasara kan ma'aurata ko masoya shakku suke fara saka wa dayansu, yana hawa shi ke nan sun cimma burinsu, domin shi zai sa duk ƙaunar da suke yi wa junansu ta wargaje. Misali namiji bai da matsala da matarsa, sai ta bar gida na tsawon sa'o'i biyar ko shida ba ta dawo ba, kuma ba  abin da zai dame shi tunda ya san aiki ta je kuma ya san kamewarta.

Da a ce zai je inda suke aiki a yi rashin sa'a ya ga ana badala to nan da nan hankalinsa zai tashi, sai ya fara bincike: "Ina kike zuwa? Da wa kuke ma'amalla? Ni fa wurin aikinnan naku ban gama yarda da shi ba, ya kamata a sami wani wurin!" Ba tare da ya gaya mata ainihin dalilin da ya sa yake son daukar wannan matakin ba. A irin wannan yanayi duk matakin da ya dauka sai an tayar da ƙura. In ya gaya mata gaskiyar lamarin matsala ne, in ma bai gaya mata ba so yake kawai ya dauke ta daga wurin nan ma wata matsalar ce ta daban. Zato ne kawai ya yi cewa komai zai iya faruwa.

To ta ya ma zai gaya mata? Ai sai ta ce yana zarginta da alfahasha ne. Wannan kenan, da a ce wani zai same shi ya kimtsa masa magana, nan ma yana iya zama matsala. Kamar ya ce "Malam ba matarka ce wance ba? Gaskiya kadan riƙa sa ido ka san duniyannan sai a hankali, kana saƙa ne wani na bi ta baya yana warware maka!" Magana ya yi a dunƙule, shi kuma zai fara saƙe-saƙe, a ƙarshe in ba a yi sa'a ba sai ka ga an kai ga zace-zace, shi ma din kan sa mutum ya ƙullaci wani irin kishi da zai ba ta tsakaninsu gaba daya.

Maza na yi, mata na yi, sai dai mata kan yi haka saboda da dalilai daban-daban. Wata ko fada ta yi da 'yar uwarta tana iya ta da kishin namiji ta wurin saka masa shakku tsakaninsa da iyalinsa. Wani sa'in kuma ta wurin iyalin ne ma za a fito, a gaya mata ƙarya da gaskiya, da zarar ta hango  abin da ba ta gane ba sai ta zaci maganar da aka gaya mata gaskiya ce, shikenan an shiga tsakaninsu. Matsalar zato ke nan ta wannan bangaren.

Maganin irin wannan kishin da zato ke kawowa yana da wahala, domin duk wanda ya ce ba zai kula duk wanda zai kawo masa gulmar iyalinsa ba, ko kuma ya ce zai dauki mataki a kansa to haƙiƙa ya bude wawukekiyar baraka a gidansa. Kamar wanda zai riƙa karbar duk  abin da za a kawo masa daidai da kuskure. Shawara kawai mutum ya karba kuma ya yi godiya, amma ya yi bincike. Ko shi binciken banda gaggawa ya bi sannu a hankali don kai wa ga  abin da yake muradi.

Wasu sun ba ta aurensu ta wurin rashin karbar shawarwarin da ake ba su kan iyalinsu. Wannan ya sa iyalin suka riƙa yin  abin da suka ga dama ba mai iya sa baki, a ƙarshe bayan lamarin ya gama tabarbarewa a dole aka balgace auren. Wasu kuwa duk  abin da aka kawo musu sai su dauka kan-jiki kan-ƙarfi, sai sun je sun yi abin kunya daga baya su ga abin ba haka yake ba su fara zargin cewa wane na neman kashe min aure. Hatta waɗanda kan dauki matakin binciken in dai ba za su bi a hankali ba, shi ma dai haka lamarin zai lalace, daya zai ce an sa masa ido, ko ana bibiyarsa ko zargi da dai sauransu.

A yi bincike amma a bi a hankali, a bi duk matakan da hankali zai iya dauka, ta bangaren matar ne ko na mijin? Allah SW ya yi hani ga bin zace-zace, ya ce wasu zace-zacen zunubi ne. To mace ma ke nan da ba ta da wani haƙƙi a kan namiji ta wurin hana shi ƙarin aure amma in ta ji yana tare da wata sai ta ta da hankalinta, to bare namijin da ya san cewa matar aure ba ta da ikon shaƙuwa da wani in ba lalata za ta yi ba, dole in mai kishi ne ya ta da hankalinsa. Amma in za a yi bincike a hankali an gama.

Na ji mutumin da wani ya taso tun daga Saminaka har Kaduna don dai kawai ya gaya masa cewa budurwarsa ta taba yin wasan fajirci (Blue film), mutumin ya sami wani malami ya tambaye shi "Kana son ta?" Ya ce i amma ai ga  abin da aka ce, ya ce "Kana ganin har yanzu tana yi ne?" Ya ce a'a amma ai ta taba yi kuma yaransu za su taso su gani. Ya ce bai ƙi ra'ayinsa ba, amma ya ba shi 'yan shawarar ya riƙe matarsa yana ladar shiryar da ita, in ya bar wa mutanen banza ba za su gyara halinta ba, mutumin kirki ne kawai zai iya haka, kishi yake kuma a wurin namiji ado ne. Ya san komai amma da aka sami wanda ya kawo mishi maganar sai ga shiri zai lalace.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments