2) ZARGI: Yakan taso ne kuma ya yi tasiri ga zamantakewar da ke tsakanin mutum biyu a lokacin da dayansu yake ganin cewa abokin tafiyarsa na boye rashin gaskiya game da alaƙar dake tsakaninsu ta aure ko ƙauna kafin auren bisa wasu hujjoji marasa kan gado da ya riga ya tattara daga ƙusurwoyi daban-daban. Daganan kuma mutum ya sami aikin yi ke nan ta yadda zai rabu da hidundumunsa masu mahimmanci ya koma bibiyan abin da inda zai same shi hankalinsa sai ya fi na kowa tashi.
Za ka ga mutum
na maida hankalinsa kan abin da masoyi
ke cewa, ba don fahimta ko yarda ba, kuskurensa yake nema wanda zai kai shi ga abin da yake zarginsa da shi. Ba maganarsa
kadai yake bincika ba har da kai-komonsa bayan a jiya ba wanda ya fi yarda da
shi kamarsa a duk fadin duniya. Ƙila a ce ƙauna ta jawo haka, amma fa in ya
samo abin da yake nema to rabuwarsu
kenan. Tunda kishi zai hana shi ganin alkhairan masoyinsa, ya dauko ƙiyayya ya
yi gilashi da ita. Wani ya yi duka, wata ta yi ƙone-ƙone ko kisa, wani ya saki.
3) TUHUMA:
Duka dai kishi ke sa sashi ya fara tuhumar sashi da cewa yana kallon wani, da a
ce mace za ta ce "Yadda Daushe yake wasa a shirin Arewa24 na Gidan
Badamasi yana burge ni don shi nake kallon shirin!" In ba a yi sa'a ba
daga ranar an daina kallon shirin ke nan a gidan, maigidan zai fara tuhumarta
da cewa tana son Daushe, wata ƙila kuma ko a hanya suka hadu ba dole ne ma ta
gane shi ba. Ta yuwu a wannan wasan ne ma kawai inda yakan ce "A bi duniya
a sannu, ga shi ba shi da gaskiya a cikin gidansa shi ma kansa ba ya bin
duniyar a sannu". Miji ba zai kalli wannan ba, kawai tana son Daushe don
haka an daina kallonsa sai dai wata tashar. Wannan kishi ne.
Ita kuwa mace
takan fara ne da zura wa mutum ido ta gani ko yana kallon wata, bare ya taimake
ta, nan take za ta yi ƙoƙarin sanin dalilin da ya sa ya yi hakan, ko ta sanin
ma dole dai komai ya tsaya daganan don kar ya kai inda ba a so, in kuwa a bayan
idonta aka yi labari ya iske ta to zargi zai iya shigowa ciki, sai tuhuma ta
fado "Me ya sa ka ba wance kaza? In don Allah ka yi ba mata ne a duk fadin
duniyannan sai ita?" Tambayar wai ba matan aure ne mai ya sa sai maras
miji? Na taba ganin wani mutumin da ya tausaya wa wata mata a cikin motar haya.
Ya saya wa matansa Multina ne mai sanyi saboda a ganinsa zai dan sassauta musu
tsananin zafin da suke ciki.
Ganin matar na
tare da matansa sai ya saya mata guda daya ya miƙa mata, nan take matarsa ta ƙwace
ta galla masa harara, amma da ta je miƙa wa matar sai ta saki fuska tana yi
mata murmushi. Tabbas ta fahimce ta amma ya za ta yi? Ta karba ta yi godiya, ko
iya kallon mijin matar ba ta yi ba bare ta yi masa tasa godiyar, zargi ya riga
ya kurdado tsakiya ba yadda za a yi, duka sun san juna, a yadda na san maza
wannan kisar macijin mata ne, an kashe ba a sare kan ba, zai farfado ya ci gaba
da tafiya sai yadda hali ha ya yi. Don wani lokaci daga irin haka ƙaunar ke
shukuwa.
4) RASHIN GANE
MUTUM: Idan mace ta fara ganin wasu abubuwan da ba ta saba gani ba, ko kuma ta
ga ana yinsu amma ba a lokacinsu ba. Misali, kwalliyar namiji da safe yake
yinta lokacin da zai fita aiki, in ba haka ba to akwai wani abu na masamman
kamar daurin aure ko wani sha'ani wanda zai halarta, in ta ga yana shan adaka
da daddare tabbas za ta fara shan jinin jikinta, bare kuma ta ga yana fesa
turare, ko yana zaben kaya da kansa bayan ita ke zaba masa, ko ya fara makarar
dawowa gida ba tare da wata ƙaƙƙarfar hujja ba, ko kuma ya fara yi wa wata kyauta
ba gaira ba dalili, masamman in ba ta da miji.
Duk wadannan
abubuwa ne da za su sanya mace cikin dimuwar cewa da walakin wato goro a miya.
Akwai matar da mijinta ya sami halin da zai ƙara gini, tun da ya fara kawo bulo
gidan aka fara samun dauki ba dadi, duka dai kishi ne wanda ya taso daga rashin
gane halin da maigida ko saurayi yake ciki a dalilin wasu abubuwa da ya ƙirƙiri
yinsu na ba gaira ba dalili. A irin wannan halin sai mace ta yi haƙuri don in
ma yana shakkarta da zarar ta matsa masa zai fito sarari ya ce mata aure yake
nema sai me? Kuma shikenan an gama.
Koda yake
akwai abubuwa da dama waɗanda suke saka mace kishi kamar kyau idan ta ga wace
ta fi ta kuma ba ta da miji, ko wani matsayi na wurin aiki ko dai na al'umma
gaba daya, ko ta fi ta karatu tana da kwali babba, ko tana aikin gwamnati ga
albashi mai tsoka ita ba ta kai nan ba, ko ta gan ta da babbar mota ko waya ta
hannu da dai sauransu duk za su iya saka ta kishi da ita, sai in ta san cewa ta
ko'ina ba yadda za a yi mijinta ya yi sha'awarta. Kishin mace ga wata a matakin
farko ba wai hassada ba ce, kar dai a ce wata alaƙa ce ta kurdado tsakaninta da
maigidanta, ba ta damu ba in za ta auri kowa amma banda maigidanta.
Anan Zan
Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.