Ticker

KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 21

8} BINCIKEN KAYA: Asalin rayuwar miji da mata ko masoya babu wata matsala, amma lokacin da iyalin za ta fara saka hannunta a aljihun jakar mijinta ba da niyyar daukar kudi ba me take nema? Wata ta taba zuwa irin wannan binciken ƙarshe ta koma gida tana kuka wai ta ga robar maza (condom) a cikin jakar mijinta, ta je da shi wurin mamanta tana tambayarta  abin da mijin yake yi da shi? Uwar ta ce "Kin bar shi a gida kika zo tambayata anan, wace iriyar amsa kike so na ba ki?" ko da yake maman ma ta damu sai dai ba nan ya kamata yarinyar ta kawo kuka ba, ta yi bincike tukunna, alabashi in akwai buƙatar kuka da tashin hankali sai ta yi da hujja.

Yadda namiji bai ƙaunar ganin wani sabon abu na maza wanda ba nasa ba a gidansa haka mata in suka ga baƙon abu na mata shakku kan shigo, a ƙarshe a ƙare da zargi, me ya kawo wannan? Ta yaya ya shigo? Sai dai akwai buƙatar a bi a hankali, akwai wani mutum da ya dawo gida ba lokacin da ya saba ba sai ya hango kamar takalmin maza a ƙofar dakin matarsa, yana kusantowa sai ya ji ana rada, nan take ya fada dakin sai ga matarsa ta yi daurin ƙirji ba ko riga, ga wani ƙato kusa da ita, kan ka ce haka har ya cafe shi ya tiƙa da ƙasa. Nan take ta ce "Danka ne Alhaji".

Koda dansa ne me zai kawo shi dakin matarsa tunda ba mahaifiyarsa ba ce? Ga shi kuma suna wata iriyar hira kusa da juna ba ta da riga? Ashe dai danta ne na fari da ta haifa a wani gidan, ba ta son ya riƙa zuwa gidan ne shi ya sa bai san shi ba, ta lura yana da kishi ko 'ya'yansa ma na cikinsa, a ƙarshe da komai ya bayyana sai ya fara fada yana tura wa matar laifin abin kunyan da ya faru wai ita ce ba ta nuna masa shi ba. Da yake abin ya yi tsanani dole sai da ya jawo yaron a jiki ya yi masa kyautar manta-uwa don dai ya goge baya.

Tabbas ya yi kishi amma akwai dalilin da ya jawo hakan. Ko me zai faru a riƙa kiyaye  abin da zai kawo zargi tsakanin masoya ko ma'aurata, duk wanda matarsa za ta dawo ya je yana shinshina kayanta ko zai ji ƙamshin wani turaren da bai san shi ba ba na zaton cewa kishi yake kawo haka, a ganina zargi ne kawai. Tunda zai yi wahala a ce yana bincike ne ko zai ji ƙamshin wani turare wanda ba shi ya sayo ba ya tambaye ta dalilin da ya sa take fesa turaren wani ba nasa ba.

Wani fa duk kayan da matarsa ke sakawa yana sane da su ya san lokacin da ya kawo su, in ya ga ta saka wani daban sai ya bi ba'asi ya ji ta inda ta samo su. Amma kamar mace kishinta ko ba dalili za ta yi abinta. Na taba ganin wani mutumin da ya sa wa kansa ja-baki sannan ya kama hanyar gida, ƙoƙarinsa kawai ya dago kishin matarsa. Ya ce dai ya yi nasara amma ko me ya sa ya yi haka wallahu a'alam. Mace kamar namiji ce in ta ga wani na 'yar uwarta mace a hannun maigidanta sai ta san ko na waye, da kuma dalilin da ya sa wannan abin ya isa hannunsa.

9) KAYAN SAKAWA: Wannan dama sai mace, namiji ba  abin da ya hada shi da kayan mace, in ya fara bi don gano wani abu to ƙila dama yana da wani labari ne da bai natsu da shi ba, a maysayinsa na maigida mai kishin iyalinsa dama wannan ya kamata, amma mace ta fara wannan za a iya cewa kishi ne sai dai ba zai haifar da da mai ido ba. Don  abin da za ta binciko in ta samo shi damunta zai yi kawai, namiji na da damar tara mata sama da daya haƙƙinsa ne wannan ba za ta iya hana shi ba.

Koda yake bincike ba laifi ba ne, addini ma ya kwadaitar da yin sa a wasu abubuwa. Amma a kiyayi  abin da zai kai ga zargi, wai ma tunda ita kadai ce a wurin mijinta binciken me za ta yi? Akan yi ne dama don gano wata matsalar dake boye a ƙarshe sai a yi ƙoƙarin maganinta kafin ta fanƙama, in mace ta san mijinta ba lalatacce ba ne ai yana da hurumin da zai ƙara aure ba matsala ba ne in ya nemi wata, binciken da mace za ta yi a kai ne matsala, don zai kai ta ga mummunan kishin da muke magana.

Namiji kuma zai ƙara aurensa ba  abin da zai hana shi, to meye amfanin binciken? Na taba ganin wata matsala da wata matar ta titsiye mijinta wai ta ga jan-baki a rigarsa alhali ita kuma ba ta saka ba,  abin da zai ba ka dariya mutuminnan na da wasu matan, ba zarginsa take da alfahasha ba, kawai dai tunda ranar girkinta ne akwai yuwuwar ya yi satar kwana kishi ke nan ko? To in ta gano me za ta iya yi a wannan lokacin?

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba


Post a Comment

0 Comments