Ticker

KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 23

11) TAKUNKUMI: Ma'anarsa anan shi ne ƙoƙarin da masoyi kan yi don hana masoyiyarsa gudanar da wasu abubuwa na ƙaruwa a waje saboda dalilansa na masamman. Wannan yana da fadi sai dai a taƙaita kan abubuwa guda biyu kacal: Akwai killacewar da za a yi wa mace ta yi amfani da wace ta zama dole a guje ta. A lokacin da mace ta fara girma gabobinta na sha'awa duk suka bayyana ya zama dole masoyi masamman wanda bai shirya ba ya shiga fargaba, don wanda ya fi shi ƙarfi zai iya buge shi ya dauke ta matuƙar bai aure ta ba shi.

Mafita kawai shi ne a san yadda za a yi a boye gabobin da za su fisgo hankulan maza, in kuwa budurwa ta kai manzilin da ba za ta iya boye komai ba to sai dai a rage hada-hadarta a gaban mazan. Misali: Wani matashi ne ya so yin auren zumunta aka yi sa'a duk bangarorin guda hudu sun yi ittifadi kan lamarin, wato masoyan da uwayensu, sai ya sami karatu a ƙasar waje ba zai iya aure ba a lokacin bare a yi maganar ya tafi da ita. Mafitar kawai a killace ta a gida a hana ta fita kwata-kwata, an haƙura da maganar karatu shi ke nan ba yadda za ta hadu da samari ko ƙawayen da za su hure mata kunne.

Wannan kishi ne amma mai kyau, sun iya tsare ta cikin yardar Allah har saurayin ya dawo ya iske ta ya aure ta. Ba wannan kadai ba, inda saurayi zai hana budurwarsa zuwa wata makaranta da hujjar maza na gwamatsuwa da mata shi kuma ba zai iya jure ganinta da wani namiji ba, tun a lokacin yana da damar da zai nuna mata manufarsa. Gaskiya yana da kishi ba zai yi jimirin ganinta a cikin maza ba. Tun daganan ita ma za ta gani in irin mijin da za ta iya aure ne ko a'a, shi ma in ya hana ta ta ƙi hanuwa zai gane ko za su iya tafiya tare ko a'a.

Maza kala-kala ne kowa da irin tunaninsa. Mun zauna da wasu matan wadanda maigidan ya ce zai iya biyan kudin makarantarsu ko a ina za su yi karatun, amma sharadinsa ba wata mace da za ta yi aiki a cikinsu. Wannan dalilin ya sa suka ce to ai karatun bai da amfani, sai suka fasa.Wata maigidan ya gaya mata hakan ta yarda ta yi karatun, da ta gama ta zauna gida. Zuwa wani lokaci ya girma ga rashin lafiya ga yara na buƙatar taimako. A wannan lokacin ya yarda ta yi aiki don taimakon gidan.

Abinda muke ƙoƙarin fitarwa a ciki kishi ya hana shi yarda a baya, yanzu ƙila ta girma ga yara sun mamaye ta gaba da baya ba ya tsoron faruwar wani abu. Na san wata yarinya mai matuƙar ƙoƙarin karatu, malaman na jinjina wa ƙoƙarinta don ita ke zama ta daya a makarantarsu, aka cire ta ta auri wanda bai damu da karatun yara ba ma bare nata. Ƙarshe dai haka ya kulle ta a gida, ya ce shi ba zai yarda ta riƙa haduwa da maza ba. Shi ma in aka lura sosai anan kishi ne ya hana karatun.

Duk wadannan ina ganin sauƙinsu. Wanda ya fi damuna shi ne wanda maigidan zai hana ta ta yi sana'a a cikin gida ma ba a waje ba, kuma ba zai wadata ta da abubuwan da take buƙata ba. Kishi na gaskiya mutum ya wadata iyalinsa yadda ba za ta yi marmarin rabuwa da shi ba ko ta yi kwadayin  abin da yake hannun wani. Ƙoƙarin yanke alaƙar mace kakab da kowa kamar tilasci ne, a yi mata yadda ita da kanta za ta rabu da kowan. Koda mutane za su shekara suna cewa ana cutar da ita ba za ta damu ba don ta san ba haka ba ne.

Kishi maras amfani shi ne wanda mutum ba likita ba, kuma matarsa na da ciki ya ce ba za ta je asibiti ba tunda maza ne za su duba ta. Na taba magana da wani a asibiti ni ma matsalata ta kai ni, na kawo ne don wasu su hankalita. Ya ga likita kuma an tabbatar masa da cewa infections sun yi musu yawa tunda har sun raunana shi. Likitan ya ce ya kawo sauran matan za a bincika. Mutumin ya ce a'a sai dai infections din su kashe su, amma matansa ba za su zo ya riƙa yi musu tambayoyin da za su shafi shimfida ba.

Wani kuma ƙin kai matar asibiti ya yi wai maza ke karbar haihuwa, abin haushi kuma ba zai iya karba ba shi, bai san kuma inda zai sami mace unguwar zoma ba. Kishi na iyali abu ne mai kyau amma in ya kai ga zai tabi rayuwa to a haƙura ya fi. Akwai macen da na sani maigidan ya yarda abokinsa likita ya yi mata wankin ciki, amma matar ta ƙi yarda, shi maigidan yana dan neman sauƙi ne tunda nan kyauta za a yi masa. Ƙarshe dai allura aka yi mata da hankalinta ya gushe aka yi aikin.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments